Ƙaƙa-tsara-ƙaƙa: Wasu daga cikin Gwamnonin APC a Arewa ba su yarda cewa sai ɗan takarar Arewa kaɗai zai iya kayar da Atiku Abubakar, ɗan takarar PDP ba.
Aƙalla Gwamnoni 9 na APC daga Arewa na ta gaganiyar ganin cewa sauran gwamnoni sun amince a bai wa ɗan Kudu takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin APC, a zaɓen 2023.
APC dai ta na da gwamnoni 14 a Arewa, sannan kuma ta na da 8 a Kudu, kuma ɓangarorin biyu na ta kashe rana da dare su na taro a asirce, domin ganin an fitar da ɗan takara ɗaya tilo, kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke so a yi, ba tare da an gwabza wajen zaɓen fidda gwani ba.
A ranar 6 zuwa 8 Ga Yuni ne APC za ta fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa, daga cikin mutum 23 da aka tantance.
Amma kuma APC ta ruɗe ganin yadda PDP ta fitar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar ta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023
Wannan ya sa wasu ke ganin cewa ɗan takara daga Kudu na APC ba zai iya kayar da Atiku Abubakar ba.
Dalili kenan wasun su ke so a bai wa ɗan Arewa tikitin takarar APC na zaɓen shugaban ƙasa, kamar yadda PDP ta yi.
A ranar Lahadi Shugaba Buhari ya gana da Gwamnonin APC 22, inda ya nemi su yi masa alfarmar ƙyale shi ya zaɓi wanda zai zama halifan sa.
Wannan ya sa gwamnonin APC sun yi taro har sau biyu a ranar Talata, domin su fitar da mutum ɗaya, amma lamarin ya faskara.
Gwamnonin sun haɗa da Babagana Zulum Borno, Simeon Lalong Plateau, Nasir El-Rufai Kaduna Abdullahi Ganduje Kano, Aminu Masari Katsina, Abubakar Bello Niger, AbdulRahman AbdulRazaq Kwara, Abdullahi Sule Nasarawa Bello Matawalle, Zamfara.
Matsalar Fitar Da Ɗan Takara Ɗaya Tilo:
Yayin da bayan abu ya faskara, gwamnonin sun amince cewa na Arewa su je su fitar da ɗan takara daga Arewa, su ma na Kudu haka. Daga nan su ka ce sai a kai wa Buhari sunayen su ya zaɓi na zaɓe.
Kada a manta, akwai Gwamnoni 3 da a yanzu haka ke cikin ‘yan takarar shugabancin ƙasa. Kayode Fayemi na Ekiti, Ben Ayade na Kuros Riba da David Umahi na Ebonyi.
Bayan jawabin da Buhari ya yi na neman a bar shi ya fitar da wanda zai zama halifan sa, bayan taro, Gwamnonin APC sun rankaya Gidan Gwamnatin Kebbi da ke Abuja, wajen ƙarfe 8 na dare, a ranar Talata. Sun kashe dare su na waswasi da ƙumbiya-ƙunbiyar shin ɗan Arewa za a fitar ko ɗan Kudu?
Dukkan Gwamnonin Arewa 14 na APC sun halarci taron, banda Nasir El-Rufai na Kaduna, wanda Mataimakiyar sa Hadiza Balarabe ta wakilce shi.
Wani magulmaci daga wurin taron ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa Gwamnoni 9 daga cikin 14 na Arewa sun tsaya lallai sai a fitar da takarar shugaban ƙasa daga Kudu, domin hakan shi ne adalcin zamantakewa da ɓangarorin ƙasar nan daban-daban.
Wasu daga cikin gwamnonin sun ce ba su yarda da cewa wai ɗan takarar APC daga Kudu ba zai iya kayar da Atiku Abubakar na PDP ba.
Gwamnonin Da Ke So APC Ta Bai Wa Ɗan Kudu Takarar Shugaban Ƙasa:
Babagana Zulum na Barno, Simeon Lalong na Filato, Nasiru El-Rufai na Kaduna da Abdullahi Ganduje na Kano.
Sauran su ne Aminu Masari na Katsina, Abubakar Bello na Neja, Abdulrahman AbdulRazaq na Kwara, Abdullahi Sule na Nasarawa da Bello Matawalle na Zamfara.
“Gwamnonin Kwara, Kano da na Katsina ba su zafafa sosai kan matsayar su ba. Amma dai su na goyon bayan a bar wa ɗan Kudu, kuma sun yarda da cewa a mutunta cika alƙawarin yarjejeniyar bin tsarin karɓa-karɓa da aka yi a baya, lokacin da aka tsayar da Buhari a 2014, cewa bayan shi dai kuma ɗan Kudu.
Gwamna El-Rufai, Zulum da Lalong sun fi ɗaga murya sosai su na nuna goyon bayan a bai wa ɗan Kudu takara kawai.
Sai dai kuma gwamnonin su 9 ba su cimma matsayar ɗan takarar da za a tsayar daga Kudu ba, “saboda akwai ‘yan takara da dama daga Kudu.
“Yayin da Ganduje ya fito ɓaro-ɓaro ya ce a bai wa Tinubu, Lalong ya ce a bai wa Rotimi Amaechi. Shi ma Gwamnan Neja ya fi son a bai wa Tinubu takara.
Amma shi Gwamnan Nassarawa ya fi son a bai wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo.
Gwamnonin APC Na Kudu Sun Haɗe Kai:
Su kuwa Gwamnonin APC 8 na Kudu dama sun ce tilas sai dai a bayar da takara ga Kudu. Amma su ma sun kasa cimma matsaya ɗaya kan wanda su ka zaɓa a bar wa takarar.
Fayemi, Ben Ayade da David Umahi duk Gwamnonin APC ne na Kudu, kuma duk su na cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa da aka tantance.