Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar fitaccen ɗan siyasar nan Abdulkarim Abdulsalam, wanda aka fi sani da suna A.A Zaura.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da labarin yin garkuwar da ita a ranar Litinin ɗin nan.
Zaura shi ne ke takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, bayan ya yi ƙoƙarin neman takarar gwamnan Kano bai samu ba.
Maharan sun arce da mahaifiyar sa mai suna Laure Mai-kunu a ƙauyen Rangaza, cikin Ƙaramar Hukumar Ungugo da ke kusa da Kano.
Kiyawa ya ce tuni aka baza zaratan jami’an Operation Puff Adder domin su ceto gyatumar Zaura, mutumin da ya yi fice wajen bayar da talalfi, agaji da taimako ga marasa galihu.
Wannan garkuwa ita ce ta baya-bayan nan a Kano, bayan kisan mutum bakwai da ‘yan bindiga su ka yi a yankin Takai, a wani gari Karfi, har su ka kashe dagacin ƙauyen.