Gwamnan jihar Barno, Babagana Zulum.ya maida wa ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP, Mohammed Jajeri martani, bayan ya ce Zulum ne ɗan siyasa mafi sauki da zai iya kada wa a zaɓen gwamna.
Kakakin gwamna Zulum Isah Gusau ya bayyana cewa badun badun ba da ba su maida wa ɗan takarar martani ba saboda shi bai kai su ɓata bakin su wajen bashi amsa ba.
Gusau ya ce ” Mutumin da aka sani shine aka magana da shi ba wanda ba a sani ba. Wa ye yasan wani Jajeri. Ko a jam’iyyar PDP ma ba san ko shi waye ba. Ƴan jam’iyyar ma basu san shi ba
” Jajeri na ta ɓaɓatu ne domin yayi suna kawai amma wa ya san shi ma. Kawai dai bari mu kira sa da ɗan takarar da ba a sani ba da yake neman suna da ƙarfin tsiya.
Idan ba a manta ba, Jajeri ya ce kada Zulum a zaɓen gwamna a jihar Barno shine abu mafi sauki a gareshi a siyasar sa.
” Ni fa tun kafin 12 na rana mun fara bukin kada Zulum a jihar Barno.
Bayan haka ya ce shi sabanne ne kuma fitaccen ɗan siyasa wanda jam’iyyar APC ke shakka, amma zai lallasa su a zaɓe mai zuwa.