Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna sun kashe ‘yan bindiga 4 sannan sun kama wata mata daya dake yi wa mahara safara makamai a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Muhammed Jalige ya sanar da haka ranar Alhamis.
Jalige ya ce jami’an tsaron wanda suka hada da rundunar ‘Special Tactical Squad Force Headquarters (STS)’ daga Abuja da rundunar ‘Operation Yaki’ sun yi batakashi da ‘yan bindigan a Saminaka dake karamar hukumar Lere ranar Laraba.
“Jami’an tsaron sun kashe ‘yan bindiga hudu a hanyar Jos zuwa Saminaka da misalin karfe 6:30 na safiyar Laraba inda daga hango jami’an tsaron ‘yan bindigan dake cikin mota kiran Sharon da wani daga kauyen Vom jihar Filato James Dawi mai shekara 31 ke tukawa suka fara buɗe wuta.
“Da dama daga cikin maharan sun gudu da raunin bindiga a jikinsu amma jami’an tsaro sun kama wasu mutum hudu da suka ji rauni a jikinsu inda bayan an kai su asibitin Barau Dikko likitoci uka tabbatar musu cewa sun mutu.
“Jami’an tsaron sun kama mace daya dake tare da maharan, mota daya kiran Sharon, bindiga daya kiran AK47 dake dauke da harsasai shida, bindiga Kiran AK-47 guda biyu, harsashi daya da harsasai da dama dabam-dabam.
“Sakamakon binciken da jami’an tsaron suka gudanar ya nuna cewa wannan mata da suka kama tare da maharan na safarar bindigogi ne wa mahara.
Jalige ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar bincike domin kamo sauran maharan sannan ya yi kira ga mutanen yankin da su rika taimakawa ƴan sanda da bayanan sirri domin samun nasarar damke waɗannan mutane.