Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyu cewa za ta rufe rumbun ta na intanet, wanda ta ke tattara sunayen ‘yan takarar zaɓukan 2023 a ranakun 17 Ga Yuni da kuma 15 Ga Yuli.
INEC ta ce za ta rufe karɓar sunayen ‘yan takarar masu zaɓen shugaban ƙasa, mataimaki, sanatoci da na tarayya a ranar 17 Ga Yuni, sai kuma sunayen ‘yan takarar gwamna da na mataimakin sa da kuma sunayen ‘yan takarar majalisar dokoki, waɗanda za a rufe a karɓar su a ranar 15 Ga Yuli.
Shugaban INEC Mahmood Yakubu ne ya yi wannan gargaɗin a lokacin da ya ke ganawa da Kwamishinonin Zaɓe na Tarayya, ranar Alhamis a Abuja.
Yakubu ya tunatar da su cewa an kammala zaɓukan fidda-gwanin dukkan jam’iyyun da za su shiga takarar zaɓen 2023 tun a ranar 9 Ga Yuni.
“INEC na buƙatar a damƙa mata sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimakin sa da na Sanatoci da Mambobin Tarayya daga ranar 10 Ga Yuni zuwa Juma’a 17 Ga Yuni.
“INEC na buƙatar sunayen ‘yan takarar gwamna da mataimaki da sunayen ‘yan majalisar dokoki daga ranar 1 Ga Yuli, zuwa 15 Ga Yuli.
“Za a loda sunayen ne a cikin rumbun tattara sunayen ‘yan takarar zaɓen 2023 na intanet, wato ‘portal’.”
Yakubu ya ce INEC na buƙatar jami’ai huɗu na daga cikin kowace jam’iyya 18 da za su yi takara su loda sunan ɗan takarar su a cikin rumbun tattara sunayen.
Yakubu ya ce tuni INEC ta damƙa wa kowace jam’iyya lambobin ɗan makullin da ake buɗe rumbun da su, domin su shiga su loda sunayen ‘yan takarar su.
“Mu na ƙara jaddada cewa sai sunayen ‘yan takarar da su ka yi nasarar lashe zaɓen fidda gwani bisa tsarin da Sashe na 84 na Dokar Zaɓe ta 2023 ne kaɗai za a loda sunayen su a cikin rumbun.”