Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a ƙarkasahin jam’iyyar PDP, Isah, Ashiru ya yi kira ga gwamnati jihar har Kaduna ƙarkashin gwamnan jihar Nasir El-Rufai da ya dakatar da korar ma’aikata da yake yi a jihar.
Idan ba a manta ba, gwamnatin El-Rufai ta kori malaman makarantun firamare a jihar ciki har da shugaban kungiyar malamai na kasa wanda ɗan asalin jihar ne.
A wata ‘yar gajeruwar sako, Ashiru ya soki hakan yana mai cewa a wannan lokaci da talaka ke ‘hannu baka hannu kwarya’ bai kamata a ce an gallaza masa irin wannan azaba ba na korar aiki da rana tsaka
” Ina talakan Kaduna zai saka kansa a halin da ake ciki, ana fama da talauci da wahalhalun rayuwa sai kuma a wayi gari wai kuma ɗan aikin da kake samun taro sisi, an kore ka, hakan da me yayi kama tsakani da Allah?
” Ina kira ga Nasir El-Rufai da ya dakatar da korar ma’aikata da yake cigaba da yi, Al’umma jihar Kaduna a halin yanzu suna fuskantar matsaloli rayuwa dabam dabam, idan ba’a tallafa musu ba to bai kamata ace ana raba su da aiyukan da suka dogara dasu don ciyar da iyalan su ba”.
Mazauna jihar Kaduna da wasu da korar ya shafa sun yi tir da wannan mataki da gwamnatin Nasir ya ɗauka a wannnan lokaci da ake fama da matsi.