Hukumar Kwastam dake kula da shiyar ‘zone D’ ta kama kayan da gwamnati ta hana shigowa da su da suka kai naira miliyan 126.560 daga watan Janairu zuwa Yuni.
Shiyar ‘zone D’ itace ke kula da jihohin Bauchi, Gombe, Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Filato da Nasarawa.
Shugaban shiyar Adesanmi Omiye ya sanar da haka ranar Alhamis a garin Bauchi.
Omiye ya ce kayan da hukumar ta kama sun hada da buhunan shinkafa masu nauyin kg 50 guda 605, motoci 7, gwanjon kaya 54, katan 215 na sabulu da katan 42 na taliya.
Saura sun hada da busassun fatocin jakkai 102, buhuna 69 na gwanjon takalma, jarka 150 na manfetur da sauran su.
Omiye ya ce shiyar ta samu wannan nasara a dalilin gudanar da bincike, hada hannu da mutane domin samun bayanai da zage damtse wajen ganin an hana aiyukkan ‘yan sumogal.
Ya yi kira ga mutane da su ci gaba da hada hannu da hukumar domin ganin an hana aiyukan ‘yan sumogal a shiyar.
“Hana aiyukan ‘yan sumogal zai taimaka wajen inganta tattalin arziki ƙasa da kawar da tallauci.