Kwamishinan Tsaron Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya ƙaryata rahotannin wasu jaridun kasar nan da suka buga cewa wai ƴan bindiga sun kai hari ƙauyukan karamar hukumar Kajuru ta jirgin saman yaƙi.
Aruwan ya ce mahara ne suka afka wasu ƙauyukan karamar hukumar inda suka kashe mutane da dama sannan suka kona gidaje.
” A lokacin da maharan ke wannan baƙin aikin sai jami’an tsaro a jirgin sama suka kawo ɗauki inda suka fatattaki maharan. Amma kuma wasu kafafen yaɗa labat suka buga cewa wai ƴan bindigan sun yi amfanin da jirgin yakin sama wajen kai harin.
SUNAYEN WAƊANDA AKA KASHE
DOGON NOMA
– Ahmadu Musa
– Audu Dandaura
– Akilu Laya
– David Wasika
– Hajatu Buhari
– Nashon Buhari
– Iliya Yaki
– Javan Mairabo
– Jackson Adamu
– Nasco Victor
– Dutse Gwamna
– Joshua Amadi
– Gona Isah
– Douglas Yakubu
– Phineas Joel
– Tanimu Umaru
– Abody Iliya
– Wanzami Halidu
– Dogo Aweh
– Sunday Shittu
– Rejoice Audu
– Jedidiah Ayawa
– Jinkai Pius
– Rebecca Ayafa
– Ishaya John
– Audu Danladi
– Jibo Sule
– Yakubu Garba
– Williams Danbaba
UNGWAN SARKI
– Maikasa Kufana
– Augustine Bahago
UNGWAN MAIKORI
– Mamiya Maikori
Aruwan ya ce ” Bai kamata a ce wai kafafen yaɗa labarai na buga irin waɗannan labarai ba tare da sun tantance ba. Saboda Allah ace wai jami’an tsaron sama sun taya ƴan bindiga kai wa mutane hari ta sama ba ayi wa gwamnati da sojoji adalci ba. Ya kata a rika tantance labarai kafina buga.
Wani mazaunin ɗaya daga ciki kin ƙauyukan da aka kai wa hari ya ce maharan sun shigo a babura suka kan mai uwa dawabi.
Discussion about this post