Iyalan waɗanda ‘yan ta’adda su ka yi garkuwa da su a harin da aka kai wa jirgin ƙasa kan hanyar Abuja-Kaduna, sun koka tare da nuna firgici gami da roƙon gwamnati ta taimaka ta kuɓutar da waɗanda har yanzu ke hannun maharan a cikin daji.
Wannan sabon roƙo da su ka yi ya biyon bayan wasu rahotanni da ke nuna cewa ‘yan ta’addar sun bindige mutum ɗaya daga cikin sauran da har yanzu ke tsare a hannun su.
Iyalan dai sun kai ziyara ce ga wasu Mambobin Majalisar Tarayya a ranar Laraba, inda su ka roƙi gwamnati ta ruɓanya ƙoƙarin da ta ke yi na ganin an ceto waɗanda ke hannun ‘yan ta’addar.
Ciki makon da ya gabata ne Honorabul Bamidele Salam, ɗan PDP daga Osun, Mansur Soro daga APC na Bauchi, tare da wasu Mambobi 10 duk sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta ƙoƙarta ceto waɗanda ke hannun ‘yan ta’adda.
Salam da Mansur Soro ne su ka karɓi baƙuncin iyalan waɗanda ke tsare ɗin, lokacin da su ka kai masu ziyarar kai kukan su ga gwamnati, a Majalisar Tarayya, Abuja.
Da ta ke magana a madadin sauran, matar ɗaya daga cikin waɗanda har yau su na can daji a hannun ‘yan ta’adda, Matilda Kabir, babu tabbas batun an kashe wani ɗaya daga cikin waɗanda ke tsare.
Matilda ta ce abin tausayi waɗanda ke tsare ɗin sun shafe kwanaki 94 a cikin daji, su na wata irin rayuwa. Sannan su kuma iyalan su na cikin tsananin jimamin waɗanda ke tsare ɗin.
“Mun samu labari a safiyar yau Laraba cewa sun bindige ɗaya daga cikin waɗanda ke tsare a hannun su.
“Ni miji na har yanzu ya na hannun su. Ba mu san kuma wanda za su sake bindigewa ba kuma. Mu na roƙon ‘yan Najeriya su taimaka mana a kan wannan al’amari.
“Jama’a ku yi tunani irin mawuyacin halin da bayin Allah ke ciki a cikin ƙungurmin daji. Sun kai kwanaki 94 a hannun masu bindigar da su ka yi garkuwa da su. Jama’a don Allah a taimaka mana.” Inji Matilda.
Sauran waɗanda su ka yi magana a wurin sun haɗa da Aminu Usman, wanda shi ma ɗan uwan sa na can tsare a hannun su.
Bamidele da Manu Soro sun jajanya masu, kuma sun taushi zuciyar su, tare da jaddada masu cewa gwamnati za ta ceto dangin su da ke hannun ‘yan bindiga tun a ranar 27 Ga Maris.
An dai saki Shugaban Bankin Bunƙasa Manoma na Ƙasa tun tuni, sai kuma wasu mutane 11 da aka saki, bayan Sheikh Ahmad Gummi ya shiga tsakani.