Hukumar kula da makarantun firamare ta jihar Kaduna ta sallami malamai 2,357 a dalilin ƙaurace wa jarabawar gwaji da ta yi a watan Disambar 2021 a jihar.
Mai magana da yawun ƙungiyar Hauwa Mohammed ta bayyana cewa waɗanda aka sallama ba su zauna jarabawar gwaji ba wanda gwamnatin jihar yi a cikin watan Disamba.
Hauwa ta ce ” Idan ba a manta ba gwamnati ta umarci malamai a jihar akalla su 30,000 da su rubuta jarabawar gwaji amma wasu da dama suka ki yin jarabawar.
” Waɗanda suka ƙi rubuta jarabawar duk gwamnati da kore su aiki. Sun rasa aikin su kenan. Sannan kuma waɗanda suka ci kasa da maki 75 cikin 100 suma za su kama gaban su, domin sun shiga cikin waɗanda gwamnati ta fatattaka.
Cikin waɗanda ba su rubuta jarabawar ba harda shugaban kungiyar malaman firamare na kasa, Audu Amba, wanda shima an sallameshi.
Sai dai kuma shugaban ƙungiyar malamai na jihar Kaduna, Ibrahim Dalhatu ya ce kungiyar ba ta amince da korar da gwamnatin jihar ta yi ba yana mai cewa ” Mun sani cewa gwamnatin jihar za ta sallami malamai, sai ta kirkiro sake rubuta wannan jarabawa.
” Nan da nan muka garzaya kotu, kuma kulotu ta bada izinin a dakatar da wannan jarabawa amma gwnati ta yi gaban kanta.
” Mun umarci malamai kada su rubuta jarabawar amma wasu suka ƙi ji saboda tsoro. Abinda na ke so a sani shine wannan sallama da gwanati ta yi ya saɓa wa umarnin kotu saboda haka mu a wurin kamar bashi ne.
Haka shima Audi Amba, ya ce uwar ƙungiyar ta kasa za ta fitar da matsayarta game da haka ranar Laraba.
Discussion about this post