Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin rasuwar wani Daliget daga jihar Jigawa wanda ya rasu a daidai yana shirin garzayawa wurin taron gangami na zaɓen ɗan takarar shugaban kasa na APC da aka yi a farkon wannnan mako.
Baba-Buji ya yanke jiki ya faɗi ne a lokacin da ya ke yin karin kumallo kafin a fara taro.
Sai dai kuma ita kanta gawar ta sa ba ta tsallake harin ƴan bindiga na.
A ranar Talata an ɗauki gawar Baba-Buji daga Abuja zuwa Dutse, sai dai kuma tafiyar ta yanke a babbar titin Abuja-Kaduna inda ƴan bindiga suka yi wa motar da wasu motoci kwantar ɓauna suka nemi yin garkuwa da gawar mamacin.
Direban motar bai kai ga faɗawa tarkon ƴan bindigan ba ya samu ya yi juyawar ‘James Bond’ ya koma Abuja ya sake kwana sai ranar Laraba. A wannan rana ma ya hakura ne da bin ta Kaduna ya koma ya bi ta Nasarawa ya zagaya ya bulla har Dutse.
An yi jana’izar Baba-Buji a Jigawa.
Tsohon gwamnan Legas Sanata Bola Tinubu ne dai ya yi nasara a zaɓen fidda gwani na APC da aka yi daga ranar 6-8 ga Yuni.
Zai kara da ƴan takara kamar su Atiku Abubakar na PDP, Kola Abiola na PRP, Peter Obi na LP, Rabiu Kwankwaso na NNPP da dai sauran su.
Discussion about this post