Wasu gungun ƴan majalisan jihar Yobe kuma ƴan jam’iyyar APC sun bayyana goyon bayansu ga Bashir Machina wanda ya ci takarar sanata na yankin Yobe ta Arewa, kujerar da sanata Ahmed Lawan ya ke akai.
Idan ba a manta ba, sanata Lawal ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zaɓen fidda gwani wanda yazo na huɗu bayan bayyana sakamakon zaɓen.
Bola Ahmed Tinubu ne ya yi nasara a zaɓen fidda hwani wanda zai gwabza da tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar a zaben 2023.
Sai dai kuma ba a nan gizo ke sakar ba domin Bashir Machina wanda shine ya fito takarar sanata na kujerar Yobe ta Arewa ya ce ba zai janye daga takarar sanata ya mika wa Lawal kujerar ba.
Hakan ya sa wasu da dama da ga mazaɓar sanata Ahmed Lawan ke ganin sanatan ya hakura hakanan ya bari wani ya ɗana shima.
“Abinda ya sa muke goyon bwyan Bashir Machina shine, tsakani da Allah dai Ahmed Lawal yanzu shekarun sa 23 yana Abuja yana wakiltar mutanen Yobe ta Arewa. Ya kamata ya hakura tunda tun farko bai ma siya fom din takarar ba, na shugaban kasa ya siya.
” Muna gode masa bisa wakilcin da yayi mana daga wannan jiha a Abuja. Yayi shekara 8 a majalisar Tarayya sannan ya tafi majalisar Dattawa a nan ma yayi shekaru 16 kenan idan aka kai 2023.
Su kan su ƴan mazaɓar sanata Lawan, Gashua sun goyi bayan ya hakura haka nan Machina ya maye gurbin sa.
Discussion about this post