Yayin da masu goyon bayan Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas su na tsaya kai da fata cewa shi ya fi dacewa a ɗauka mataimakin shugaban ƙasa a takarar Atiku ta zaɓen 2023, wasu shugabannin jam’iyya kuwa na cewa sai dai a ɗauki Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa.
Naci da dagewar da jiga-jigan da ke goyon bayan Gwamna Nyesom Wike a matsayin wanda zai yi wa Atiku Abubakar mataimakin takara cewa sai dai a ɗauke shi, hakan ya kawo tsaikon ga Atiku wajen zaɓen wanda zai yi masa mataimaki a PDP.
Tun a ranar 29 Ga Mayu ne Atiku ya yi nasarar lashe zaɓen fidda gwani na PDP, inda Wike ne ya zo na biyu.
A ranar 17 Ga Yuni ne dai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC za ta rufe karɓar sunayen ‘yan takarar muƙamai daban-daban a zaɓen 2023.
Okowa dai ya mara wa Atiku Abubakar baya a zaɓen fidda gwani, kuma a yankin Kudu maso Kudu ya ke, inda Wike shi ma ya fito.
Yayin da aka ce hankalin Atiku Abubakar ya fi kwantawa da Okowa, amma ya kasa zaɓen sa, saboda masu matsa wa Atiku lamba sun ce zai fi kyau ya ɗauki Wike, saboda ya fi shi ginannar rumfar siyasa a ƙasar nan, kuma ya fi Okowa ƙarfin aljihu.
Masu goyon bayan Wike sun nuna yadda ya riƙa ceto PDP idan ta afka cikin rikici da kuma yadda ya ke ɗaukar hidimomin jam’iyya a jihohin da ba PDP ke da gwamnati ba.
Masu adawa da Wike na cewa gaskiya wani irin gaɓotarin mutum ne, wanda ba zai dace a ce da shugabanci ba.
Sannan kuma sun ce idan har PDP ta yi nasarar kafa gwamnati, to Wike ba shi da kimtsuwa, zai riƙa tayar da daru da raba kan mulki a fadar shugaban ƙasa.
Majiyar da ke kusa da Atiku ta ce ya yi wa Wike alƙawarin zai naɗa shi Ministan Fetur idan PDP ta yi nasara. Idan ba ya so kuwa, to shi zai kawo sunan wanda ya ke so a naɗa ministan fetur ɗin.
Sai dai kuma masu goyon bayan Wike na cewa ba su son Minista Fetur a yanzu. Sun ce “ɗinyar makaho ta nuna aljihun sa. Mataimakin shugaban ƙasa su ke so a bai wa Wike, domin wannan muƙamin ake nema a yanzu, alƙawari kuwa ba tabbas ba ne a cika shi idan an ci zaɓe.” Cewar masu goyon bayan Wike.
Atiku ya gaba da Gwamnonin APC 13 sa’o’i kaɗan bayan an bayyana Bola Tinubu ne ya yi nasarar zaɓen fidda-gwanin APC.
Taron dai da Atiku ya yi da gwamnonin, sun daɗe su na tattauna batun wanda zai ɗauka ya yi masa mataimakin takara.
Discussion about this post