Shugaban rukunin jami:ar MAAUN dake Kano da Maraɗi jihar Nijar, Farfesa Abubakar Adamu Gwarzo, ya yi wa ma’aikatan ɓangaren tsaftace jami’ar kyautar naira miliyan daya domin samun ƙarfin ƙwarin guiwa wajen aikin tsaftace jami’ar.
Ma’aikatan wanda da kansa farfesa Gwarzo yayi wa jawabi a harabar makarantar ya yaba da aikin da suke sannan ya hore su da su cigaba da yin aiki tuƙuru domin tsartace jami’ar.
Da suka jawabin godiya ga farfesa Gwarzo, wasu daga cikin ma’aikatan da suka tofa albarkacin bakunan su sun jinjina wa farfesa Gwarzo bisa ayyukan alkhairi da ya ke yi wa ma’aikatan jami’an da jama’a baki ɗaya.
” Babu abinda zamu ce sai Allah ya kara ɗaukaka kuma muna godiya matuka da wannnan karamci da kyautatawa da kake mana. Allah ya saka da Alkhairi.
” Zamu ci gaba da maida hankali a aikin mu kuma muna fata muma watarana ƴaƴan mu za su shiga wannnan makaranta domin su yi karatu a cikin sa.
Kafin a gama taro, sai da ɗaya daga cikin shugabannin ma’aikatan ya sanar da su cewa kyautar naira miliyan daya da farfesa Gwarzo yayi musu alƙawarin ba su ya shiga cikin asusun sa.
” Ina mai shaida muku cewa naira miliyan daya da farfesa yayi alƙawarin a raba musu ya shiga cikin asusun banki na.