Ƴan ƙungiyar IPOB, masu fafutikar ɓallewa daga Najeriya da kafa kasar Biafra sun jejjefa bamabamai a kasuwar Izombe da ke jihar Imo.
Kamar yadda rahotanni game da abin ya iske mu, ƴan kungiyar sun dira kasuwar Izombe da ke ƙaramar hukumar Aguta, Jihar Imo a daidai ƴan kasuwa sun buɗe shaguna an fara hada-hadar kasuwanci sai ƴan IPOB ɗin suka dira.
Bayan bam da suka jejjefa, sai kuma suka cinna wa motoci wuta.
” Muna cikin kasuwa mun fara harkokin kasuwancin mu sai muka ji tashin bamabamai, da harbe-harbe. Daga nan ne fa mutane suka fara gujeguje. A haka kuma ƴan IPOB din suka cinna wa wasu motoci wuta suka fatattaki kowa.
Majiya ta shaida cewa, ƴan ƙungiyar sun gargaɗi mutane da ƴan kasuwa cewa kada su kuskura su buɗe wannan kasuwa ranar Litinin domin dokar zaman gida dole na nan a jihar.
Kungiyar IPOB ta janye dokar zaman gida dole da ta saka a yanki kudu maso gabas. A lokacin da ta janye dokar, kungiyar ta ce za a rika zaman gida dole ne a duk lokacin da shugaban kungiyar Nnamdi Kanu zai bayyana a kotu.
Sai dai kuma duk da wannan umarni, ƴan kungiyar sun cigaba da muzguna wa mutane a duk lokacin da suka karya dokar zaman gida dole a duk Litinin ɗin kowacce mako.
Mutane ma sun hakura da fitowa a wannan rana saboda tsoron kada su afka musu.