Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma ya bayyana cewa dokar Najeriya bata hana dan takarar shugaban kasa musulmi ya zabi mataimakin dan takara musulmi.
Hakan ya biya takaddamar da ake yi ne a fadin kasar nan inda ake ta yayadawa cewa wai bai kamata Bola Tinubu wanda shine dan takarar APC kuma musulmi ya zabi mataimaki daga Arewa kuma musulmi ba.
Wasu na ganin cewa lallai ya zama dole Tinubu ya zabo mataimakin sa daga Arewa kuma Kirista. Amma kuma masu yin sharhi gane da siyasar Najeriya sun bayyana cewa abin ya kasu kashi biyu ne. Ko dai yayi abin da ya dace wato ta zabi mataimaki daga Arewa kirista kuma ya fadi zabe ko kuma ya yi abin da zai sa ya ci zabe, wato ya zabi musulmi dan Arewa ya ci zabe.
Uzodinma ya ce ‘yan kabilar Igbo a kasar nan ba su bukatar mataimakin shugaban kasa, shugaban kasa suke so kuma shine kawai abinda suke muradin samu kasar nan.
Saboda haka za su ci gaba da fafutar neman haka har Allah ta sa su dace.
Hukumar Zabe ta kasa INEC ta bayyana cewa duka ‘yan takara dole su aika da sunayen mataimakan ‘yan takarar su zuwa ranar 17 ga wata wato ranar Juma’ar wannan mako.
Discussion about this post