Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana dalilan da su ka sa ta aikata abin da wasu su ka yi wa fahimtar cewa kamar ta yi son kai wajen karɓar sunayen wasu ‘yan takarar da ake ganin cewa ba su shiga zaɓen fidda-gwani ba.
Sunan Sanata Ahmad Lawan wanda shi ne Shugaban Majalisar Dattawa ya bayyana a jerin sunayen ‘yan takarar da APC ta damƙa wa INEC. Haka ma sunan tsohon Ministan Harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio.
Lawan dai bai shiga takara sanata ba, takarar shugaban ƙasa ya shiga. Shi ma Akpabio bai yi takarar sanata ba, amma duk sunayen su APC ta miƙa, ba sunayen halastattun ‘yan takarar da su ka ci zaɓen fidda-gwani ɗin ba.
Yayin da Kwamishinan INEC na Tarayya da ke Jihar Akwa Ibom Mike Igini ya haramta sunan Akpabio a jerin ‘yan takara, shi kuwa sunan Lawal ya samu shiga kai-tsaye, duk kuwa da ƙorafi da barazanar da wanda ya lashe zaɓen, Machina ya yi.
INEC Ba Ta Da Ikon Ƙin Karɓar Sunayen Da Jam’iyya Ta Damƙa Mata – Kwamishinan Zaɓe:
A martanin da Mohammed Haruna na INEC ya yi wa marubuci Farooq Kperogi, ya bayyana cewa “INEC ba ta da ikon ƙin karɓar ko ma sunan wane ne jam’iyya ta kai mata.
“Jam’iyya ce ke da ikon gudanar da zaɓe, ita kuma INEC doka cewa kawai ta yi ta je ta sa-ido ta ga yadda aka gudanar da zaɓe, ta kai rahoto a hedikwata, idan an bi ƙa’ida ko ba a bi ba.
“Ƙarfin INEC a nan shi ne duk wanda ya kai ƙara kotu cewa an yi masa rashin adalci a zaɓen, to da rahoton mu zai yi amfani ya kai ƙara, kotu ta ƙwatar masa takarar sa.”
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da Machina ya ce canja sunan sa da na Ahmed Lawan rashin mutunci ne, zai garzaya kotu.
Bashir Machina wanda ya lashe zaɓen fidda-gwanin APC na Sanatan Yobe ta Arewa, ya bayyana cewa ya yi mamakin ganin yadda jam’iyyar APC ta maye sunan sa da na Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan a jerin sunayen da ta miƙa a Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC.
Machina ya ce ya yi mamaki, amma dai ya na fatan kuskure aka tafka. Ya ce shi ne halastaccen ɗan takarar, wanda ya shiga zaɓen fidda-gwani, kuma ya samu ƙuri’u 280, alhalin Sanata Lawan ko takara bai shiga ba.
Machina wanda tsohon Shugaban Ƙungiyar Masu Harkokin Jiragen Ruwa ta Ƙasa ne, ya ce maye sunan sa da sunan Lawan rashin mutunci ne kuma tantagaryar rashin imani ne.
Lawan dai ya yi watsi da shiga takarar sanata, ya shiga takarar shugaban ƙasa. Sai bayan da ya janye a ranar zaɓen fidda-gwani ne, bayan nasarar Bola Tinubu, sai Lawan ya zabura neman kujerar takarar sanata, ko ta halin ƙaƙa, bayan an yi zaɓe, har Machina ya hi nasara.
Dokar Zaɓe Sashe na 31 ya ce za a iya canja sunan ɗan takara idan ya mutu ko kuma ya janye don kan sa, ta hanyar rubuta wa INEC wasiƙar sanarwar janyewar.
Machina wanda ya taɓa yin ɗan majalisar tarayya a jamhuriya ta uku, ya yi gargaɗin idan ba a maida sunan sa ba, zai ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kotu.
“Ban janye ba, kuma ba zan janye wa kowa ba.
“Kuma ko da ba a maida suna na ba, idan ya shiga zaɓe, aka kai ƙara, to za a bai wa Machina haƙƙin sa.” Inji wasu lauyoyi.
Discussion about this post