A Jihar Bauchi manyan APC su shida, waɗanda su ka haɗa ‘yan Majalisa da tsohon mataimakin gwamna, sun fice daga jam’iyyar APC a jihar Bauchi. Kuma ba su kaɗai su ka fice ba, har da ɗimbin magoya bayan su duk su ka yi gaba, su ka bar APC cikin ruɗani a Bauchi.
Ficewar manyan APC daga jam’iyyar a Bauchi ya kawo cikas ƙwarai ga ƙoƙarin da ta ke yi na karɓe mulki daga hannun PDP, wadda Gwamna Bala Mohammed ya sake tsaya mata takara, domin ya kammala zangon sa na biyu kuma na ƙarshe.
Guguwar canjin sheƙa ko guguwar ficewa daga APC ba a Bauchi kawai ta tsaya ba. Hasalallu daga jihohi daban-daban na ci gaba da yin tururuwar ficewa daga APC su na shiga wasu ‘jam’iyyun daban.
Babban dalilin ficewar mafiya yawan su shi ne zargin rashin adalcin da su ke cewa an tafka masu yayin zaɓen fidda-gwani.
Hasalallun Da Suka Fita APC A Jihar Bauchi:
Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu, Lawal Gumau ya fita daga APC ya koma NNPP, bayan ya kasa lashe zaɓen fidda-gwani.
Shi ma Sanata Halliru Dauda ya canja sheƙa, bayan ya kasa cin zaɓen fidda-gwanin takarar gwamna.
Sai kuma Ɗan Majalisar Tarayya na Bauchi, shi ma ya fice bayan ya kasa cin zaɓen fidda gwani.
Tsohon Mataimakin Gwamna, Abdu Sule ya fice saboda abin da ya kira rashin dattako da rashin sanin ya-kamata da ake nunawa a APC.
Akwai Farouq Mustapha, Ibrahim Mohammed da sauran su.
Katsina: Yadda NNPP Ta Kwashi Lodin Mutanen Buhari:
Akwai Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Malumfashi/Ƙafur, Babangida Talau, Armaya’u Kado mai wakiltar Dutsin-Ma/Kurfi, Aminu Ashiru mai wakiltar Mani/Bindawa.
Hadimin Aminu Abdulƙadir mai suna Bature Ibrahim ya ce “Oga na zai sake shiga takara ya kare kujerar sa a ƙarƙashin NNPP.
Shi kuma Talau takarar Sanata ya fito a ƙarƙashin NNPP a shiyyar Sanatan Katsina ta Kudu.
Akwai tsoffin ‘yan takarar gwamna biyu, Umar Abdullahi (Tata) da Garba Ɗanƙani, duk sun fice daga APC.
Umar ya koma PDP, shi kuma Ɗanƙani takarar gwamna zai yi a ƙarƙashin AA.
A Sokoto Guguwa Ta Yi Wa APC Ɓarna:
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Gwadabawa/Illela, Abdullahi Salame ya sha kwaramniyar rikicin neman neman ƙwato APC daga riƙon laya hannun ɗan damben da Sanata Aliyu Wamakko ya yi mata. A yanzu dai Abdullahi ya koma PDP.
Ɗan Majalisar Tarayya Isa Kurdula ya koma PDP, shi ma Bello Jibrin tsohon Ministan Al’adu da Yawon Buɗe Ido ya koma PDP.
A Katsina, kwanan baya PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa ɗan’uwan Buhari ya yi rantsuwar tarwatsa APC
Discussion about this post