Dan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, jam’iyya mai alamar kayan marmari, kukam tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa Najeriya ta fada cikin halin kakanikayi musamman a harkar matsalar tsaro.
A jawabi da yayi wa wasu magoya bayan sa a Abuja, Kwankwaso ya bayyana cewa da jam’iyyar PDP da APC duk sun ragwargwabe babu abinda za su iya kawo wa talakawa a halin da ake ciki yanzu.
Ya ce ” An mai da ran mutum kamar kiyashi idan an kashe mutum an kashe banza idan an sace mutum an saci banza.
” Yanzu zancen da nake yi tun da aka je aka yi attacking jirgin ƙasa daga nan zuwa Kaduna har yanzu mutane na nan a daji.
” Wasu a wurin aka kashe su, wasu a wurin suka ji rauni wasu har yanzu su na nan a daji. Wannan ba karamin abin takaici bane.
” Kuma abin takaicin har da fa gwamnan mu na Kano janaral Idris Garba mutumin arziki mutum mai daraja wanda a lokacin kuriciyarsa ya kare kasar nan a kowani hali tun lokacin yakin basasa ta Najeriya amma yanzu an wayi gari shugabani ba za su iya kare shi ba. A yanzu zancen da ake yi ‘ya’yan sa ma na gadi.
” Yanzu juyawa ake idan ana son ka ko kai wani ne sai a je a yi shiri wurin ‘yan ta’adda a karbo ‘yan uwanka ko abokan ka. Wadannan mutum 11 a hak aka tafi. Ina gwamnati?
” Duk wani kanfe da za a yi wa mutane talakawa domin su zabi jami’yyan APC ko PDP ina fata mutane za su tambeye su cewan za su yi din amma a haka da su kadai ne ke kwashe kudin jama’a, su kadai ne ke da kariya da samun sauran ababen more rayuwa? Wannan fa itace babban matsalar da muka shiga a kasar nan.
” Idan ba mu da muke da karfi mun fito mun nemi a kawo canji a kasar nan ba matsalar zai ci gaba da tabarbare wa.
“Ina so na gaya muku cewa lalacewa ta kai lalacewa kuma shugabani babu wanda ya damu duk wanda ya ce maka ya damu karya yake yi. Kuma abin ya tafi konina musamman a nan Arewa.
” Kuna gani komai sai lalacewa yake yi tattalin arziki ya wargaje, an wayi gari ‘ya’yan mu da suka yi karatu sun kammala babu aikin yi, Da yawa na neman shiga makarantar amma babu hali.
Yanzu ‘yan ASUU da su da yara duk suna gida kuma Allah kadai ya san ranar da za su dawo Kuma babu wanda ya damu.
Wannan abubuwa na ilimi da ake shukawa yanzu ba yau ne za a ga illansu ba sai nan gaba kamar yadda abin da ake gani yanzu abubuwa ne da aka shuka su a baya.
Discussion about this post