Birnin Legas wanda shi ne tsohon Banban Birnin Najeriya kafin hedikwatar mulki ta koma Abuja, shi ne birni na biyu mafi munin zaman rayuwar jama’a a duniya.
Rahoton Ƙungiyar Nazarin Tattalin Arzikin Jama’a Kan Awon Mizanin Rayuwa a Muhalli (EIU) ya tabbatar da haka, daga cikin binciken da su ka a a cikin manyan birane 172 na duniya, a rahoton 2022.
Birnin Damashƙa, Babban Birnin ƙasar Siriya ne birni mafi munin zaman rayuwa ga al’ummar cikin ta, wanda daga shi sai Legas.
A nazarin tantancewar da aka yi dai Legas ya samu maki kashi 32.2. Daga Legas sai kuma birnin Tiripoli na Libiya. Damashƙa wato Damascus da Tiripoli duk birane ne da yaƙe-yaƙe da rikice-rikicen ta’addanci ya ragargaza.
Sauran ƙasashen da mazauna biranen wulaƙantacciyar rayuwa sun haɗa da Karachi, babban birni mafi yawan al’umma a ƙasar Pakistan. Sai kuma Algiers da ke Aljeriya.
Sauran sun haɗa da Moresby, Dhaka, Harare, Doula da kuma Tehran, Babban Birnin ƙasar Iran.
“Kamar yadda binciken baya su ka riƙa nunawa, zama a cikin mummunar rayuwa a wulaƙantaccen muhalli ya fi muni a waɗannan birane na duniya guda 10.” Haka rahoton ya tabbatar, tare da ƙara cewa, “ana ɗora birane 10 mafi munin rayuwa a cikin su a kan mizanin yaƙe-yaƙe, rikice-rikice da ta’addanci.
“Kuma birane bakwai a cikin 10 ɗin duk a nahiyar Gabas ta Tsakiya su ke da kuma Afirka.”
Rahoton ya ce birnin Vienna na ƙasar Austria ne mafi daɗin zama a yi kyakkyawar rayuwa a duniya. Daga shi kuma sai Copenhagen, Calgary, Zurich da Vancouver. Waɗannan su ne birane biyar mafi kyawon zaman ingantacciyar rayuwa a duniya.
Birnin Vienna na Austria ya zo na ɗaya ne bayan ya samu maki 99.8.
Kusan shekaru biyar kenan tun daga 2017 Legas na zuwa ta biyu wajen munin rayuwa a cikin jerin manyan biranen duniya.
Ana auna abubuwan da rayuwa ke buƙata domin inganta daban-daban a cikin biranen yayin ɗora su a kan sikeli.
Birnin Legas ne kaɗai aka ɗora kan sikelin gwajin rayuwar daga cikin sauran biranen Najeriya.
Don haka ba a iya tantancewa takamaimen wane birni ne mafi muni a Najeriya.
Discussion about this post