Wasu sahihan bayanan rahoton danne haƙƙin marasa galihu da PREMIUM TIMES ta ci karo da su, sun tabbatar da yadda Gwamnatin Jihar Ebonyi ta yi wa manyan ma’aikatan jihar watandar naira miliyan 400 na kuɗaɗen da ya kamata a ce marasa galihu ne aka raba wa tallafin korona (Covid-19) da kuɗaɗen.
Ma’aikatan da su ka ci wannan gajiyar haƙƙin marasa galihu su fito ne daga ɓangaren Majalisar Dokoki, ɓangaren Zartaswa da kuma ɓangaren Shari’a na jihar.
Wani rahoton binciken kuɗaɗe na shekara-shekara ne ya fallasa wannan wuru-wuru, wanda aka tabbatar cewa an raba masu kuɗaɗen ne a matsayin ramce domin su gina gidaje ko su mallaki filaye a wurare daban-daban.
Majalisar Dokokin Jihar Ebonyi ce ta amince a raba kuɗaɗen a matsayin tallafin korona, amma ga marasa galihu za a raba kuɗaɗen, ba ga masu maiƙo a hannu ko a cikin aljihu ba.
Majalisar Ebonyi ta ƙara kuɗaɗen a cikin kasafin ta na 2022, inda ta saka kuɗaɗen a matsayin ƙari kan kasafin 2022, a cikin Agusta, 2020.
Yayin da aka kasafta kuɗaɗen aka bai wa ɓangaren Zartaswa naira miliyan 200, an bai wa ɓangaren Majalisar Dokoki ramcen naira milyan 100. Sai ɓangaren shari shi ma naira miliyan 100 aka kasafta masa.
Ita dai Gwamnatin David Umahi ta ce ba ta aikata laifin komai ba, tunda ba kuɗaɗen ba daga kuɗaɗen tallafin korona na tarayya ne ta kwashe su ba.
Shi ma Akanta Janar na Jihar Ebonyi, Calton ya shaida cewa kuɗaɗen aka raba ɗin ba daga Kuɗaɗen Tallafin Gwamnatin Tarayya ba ne. Ya ce daga aljihun asusun Jihar Ebonyi aka raba kuɗaɗen.