Babban Jojin Najeriya Tanko Muhammad ya ajiye muƙamin sa, watanni 18 kafin lokacin ritayar sa.
Tanko dai kamata ya yi a ce zai yi ritaya a cikin Disamba 2023.
Sanarwa ta ce ya yi murabus ne saboda dalilai na rashin lafiya.
A cikin Disamba 2023 ne zai cika shekara 70 a duniya. Yayin da a yanzu shekarun sa 68.
Ba a dai bayyana irin rashin lafiyar sa ba.
Ana sa ran nan ba da daɗewa ba Shugaba Muhammadu Buhari zai rantsar da mafi girman muƙami daga cikin Alƙalan Kotun Ƙoli, wato Olukayode Ariwoola a matsayin Cif Joji na riƙo.
Tanko ya yi murabus ne mako ɗaya bayan wasu Alƙalan Babbar Kotun Ƙoli su 14 sun rubuta masa wasiƙar ƙorafin cewa ba ya jan su a jika, kuma ya fi su shan dage-dage da jar miya.
A cikin ƙorafin da su ka yi har da zargin ba ya kula da haƙƙoƙin su. Sannan kuma ya daina kashe kuɗi ana kunna janareton da ke bai wa Kotun Ƙoli wutar lantarki.
Alkalai 14 ne su ka sa wa wasiƙar ƙorafin hannu, wadda ta watsu kamar wutar-daji a soshiyal midiya.
An nada Tanko cikin 2019 kafin zaɓe, bayan Shugaba Buhari ya dakatar da Cif Joji Walter Onnoghen.
Discussion about this post