Rotimi Amaechi mutum ne da ya ci ribar dimokraɗiyya sosai, domin tun daga 1979 ya ke damawa da shi a jiha, har ya zama Gwamnan Jihar Ribas, tsawon shekaru takwas, daga 2007 zuwa 2015.
Daga 2015 kuma Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta APC, ta naɗa shi Ministan Harkokin Sufuri, muƙamin da ya riƙe tsawon shekaru bakwai.
Amaechi ya ajiye muƙamin Ministan Sufuri, ya shiga siyasa, inda ya shiga takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Amaechi ya gwabza zaɓen fidda gwani shi da ‘yan takara 17, bayan wasu bakwai sun janye a ranar zaɓe.
Ya yi ƙoƙari sosai, domin ya zo na biyu, amma ya samu ƙuri’u 316 kacal. Yayin da wanda ya yi nasara, Bola Tinubu ya samu ƙuri’u fiye da dubu ɗaya.
Masu fashin baƙin siyasa na fassara Amaechi da cewa ya yi tunanin zai samu ɗaurin gindi daga Fadar Shugaban Ƙasa, domin ya samu takara.
Shi kan sa Amaechi ya yi wasu abubuwa da su ka bai wa da dama mamakin cewa duk share hanyar neman takarar shugaban ƙasa ne ya sa Amaechi ya yi su.
Misali ya kai aikin gina Jami’ar Harkokin Fasahar Sufuri a Daura. Sannan kuma ya shiga, ya fita an naɗa shi sarautar gargajiya ta Ɗan Amanar Daura.
Ganin yadda Amaechi ya dira filin zaɓen fidda-gwani da ƙarfin sa, kamar wani ingarman doki, ya sa mutane sun yi tunanin akwai abinda ya taka.
Sai dai kuma bayan kammala ƙidayar ƙuri’u, Amaechi ya samu 316 kaɗai.
Amaechi ya karaɗe Arewa da sauran jihohin ƙasar nan ya na neman amincewar wakilan zaɓen ‘yan takara. Amma abin mamaki, 316 kaɗai ya samu.
Shin ya aka yi gwanin rawa ya faɗi? Wasu na cewa ‘deliget-deliget’ ne su ka juya masa baya.
Wasu kuma cewa su ke yi waɗanda ya dogara da su ɗin ne su ka canja masa fuska lokacin da zaɓen ya kusanto.
Yanzu dai Amaechi ba Minista, ba takara kuma babu naira miliyan 100 da ya sayi fam.
Abin da zai fuskanta a yanzu kuma shi ne Kwamiti Binciken da Gwamna Wike ya kafa masa, inda ake zargin sa da karkatar da fiye da sama da naira biliyan 80.