Wani bidiyo da ya faɗo hannun PREMIUM TIMES Hausa, ya bayyana ƙarara yadda Sanata Lawan Ahmad bai shiga zaɓen fidda gwani na Sanatan Yobe ta Arewa ba.
Baturen Zaɓe Danjuma Isa Munga, ya bayyana cewa daliget 289 sun jefa wa Bashir Sheriff ƙuri’a, duk kuwa da cewa shi kaɗai ne ya fito takara. An samu lalatattun ƙuri’u 11.
“Mun bi tsarin dokar zaɓe ne, duk da shi kaɗai ne ɗan takara, kuma kowa ya amince da shi. Duk da haka mu ka kira wakilan zaɓen fidda gwani daga Ƙananan Hukumomi shida, suka zaɓe shi.”
Zan Nemi Haƙƙi Na A Kotu -Machina, halastaccen ɗan takara:
Machina ya ce canja sunan sa da na Ahmed Lawan rashin mutunci ne, zai garzaya kotu.
Bashir Machina wanda ya lashe zaɓen fidda-gwanin APC na Sanatan Yobe ta Arewa, ya bayyana cewa ya yi mamakin ganin yadda jam’iyyar APC ta maye sunan sa da na Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan a jerin sunayen da ta miƙa a Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC.
Machina ya ce ya yi mamaki, amma dai ya na fatan kuskure aka tafka. Ya ce shi ne halastaccen ɗan takarar, wanda ya shiga zaɓen fidda-gwani, kuma ya samu ƙuri’u 280, alhalin Sanata Lawan ko takara bai shiga ba.
Machina wanda tsohon Shugaban Ƙungiyar Masu Harkokin Jiragen Ruwa ta Ƙasa ne, ya ce maye sunan sa da sunan Lawan rashin mutunci ne kuma tantagaryar rashin imani ne.
Lawan dai ya yi watsi da shiga takarar sanata, ya shiga takarar shugaban ƙasa. Sai bayan da ya janye a ranar zaɓen fidda-gwani ne, bayan nasarar Bola Tinubu, sai Lawan ya zabura neman kujerar takarar sanata, ko ta halin ƙaƙa, bayan an yi zaɓe, har Machina ya hi nasara.
Dokar Zaɓe Sashe na 31 ya ce za a iya canja sunan ɗan takara idan ya mutu ko kuma ya janye don kan sa, ta hanyar rubuta wa INEC wasiƙar sanarwar janyewar.
Machina wanda ya taɓa yin ɗan majalisar tarayya a jamhuriya ta uku, ya yi gargaɗin idan ba a maida sunan sa ba, zai ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kotu.
“Ban janye ba, kuma ba zan janye wa kowa ba.
“Kuma ko da ba a maida suna na ba, idan ya shiga zaɓe, aka kai ƙara, to za a bai wa Machina haƙƙin sa.” Inji wasu lauyoyi.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=fHxFuD8krzU&w=660&h=365]
Shugaban APC, Adamu ya ce Lawan ne ya ci zaɓen fidda gwani
Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya yi iƙirarin cewa Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya shiga zaɓen fidda-gwani na ‘yan takarar Sanatan Yobe ta Arewa.
APC dai ta miƙa wa INEC sunan Lawan ne maimakon sunan Bashir Sheriff-Machina, wanda aka bayyana shi ne ya yi nasara.
Sanata Ahmad Lawan wanda shi ne Kakakin Majalisar Dattawa, bai shiga zaɓen ba, sai ya shiga zaɓen fidda-gwani na takarar shugaban ƙasa. Shi ma ɗin ya janye wa Bola Tinubu ana kusa ga fara jefa ƙuri’a.
Bayan kammala zaɓen fidda-gwanin Sanatan Yobe ta Arewa, Bashir Machina ya yi nasara, inda aka kaɗa ƙuri’u 300 daga daliget na ƙananan hukumomi shida.
An samu lalatattun ƙuri’u 11, yayin da sauran 289 duk aka jefa wa Bashir Machina su. Dama kuma shi kaɗai ne ya fito takarar.
Bayan kwana biyu, an riƙa cewa Lawan ya roƙi Machina ya janye daga takarar, ya damƙa wa Ahmad Lawan, amma kuma ya ce ba zai janye ko ya miƙa wa Lawan ba.
Ba a san hawa ba, ba a san sauka ba, sai aka ga APC ta damƙa wa INEC sunan Lawan a matsayin ɗan takarar da ya ci zaɓen da bai shiga ba, maimakon sunan halastaccen ɗan takarar, Bashir Machina.
A ranar Litinin ‘yan jarida sun rufe Abdullahi Adamu, su na neman ƙarin bayanin yadda aka yi wa Bashir Machina juyin waina da sunan Ahmad Lawan.
Adamu ya tsaya kai da fata cewa lallai, “Lawan ya shiga wani zaɓen fidda gwani bayan na shugaban ƙasa da ya shiga.”
Ya ce babu wata dokar da ta hana ɗan takara shiga zaɓe fiye da ɗaya.
“Ban cika son amsa kowace tambaya ba, musamman idan daga masharranta tambayar ta fito.
“Wanda ke tantama sai ya je ya tambayi wanda ya shirya zaɓen fidda gwanin. Ni dai na yi iyakar nawa ƙoƙarin.
“Amma dai na tabbata cewa Lawan ya shiga zaɓen.”
Adamu bai bayyana a ina Lawan ya shiga takarar ba, bai kuma bayyana ko ƙuri’a nawa ya samu ba.
Ya yi ƙoƙarin a janye a bar wa Lawan takarar, amma sauran shugabannin APC su ka ƙi goyon bayan sa, ciki har da Gwamnonin APC.