Wasu masu zanga-zanga a jihar Legas sun koka kan yadda wani gwanin su ya faɗi zabe a zaben fidda ɗan takara na majalisar tarayya na mazabar Kosofe, jihar Legas.
Jagorar masu zanga-zangar ta ce wani ROT ne suke so amma aka yi masa ƙarfa-ƙarfa aka murɗe masa zaɓe aka baiwa wani da ba shi ne mutane ke so ba.
” Idan har ba a baiwa wanda muke so ba, ba zan zaɓi jam’iyyar APC ba a zabe mai zuwa.