Makonni biyu bayan kammala zaɓen fidda-gwanin takarar shugaban ƙasa na APC, tuni har an fara tambaya da tuninin makomar ministocin Shugaba Muhammadu Buhari, waɗanda su ka ajiye muƙaman su, su ka shiga takarar shugaban ƙasa.
Daga cikin Ministocin Buhari, waɗanda su ka shiga takarar sun haɗa da Karamin Ministan Ilmi, Emeka Nwajiuba, Ministan Harkokin Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, sai Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi da kuma Ministan Harkokin Bunƙasa Yankin Neja Delta wato Godswill Akpabio.
Sun lale Naira miliyan 100 kowanen su ya sayi fam na takara. Yayin da wasu sun janye ana kusa da fara zaɓe, Amaechi bai janye ba, ya samu ƙuri’u 316, kuma shi ya zo na biyu.
Akpabio ya janye daidai lokacin da ake shirin fara zaɓe. Sai dai kuma wakilan zaɓen ‘yan takara na jihar Akwa Ibom su 91 ba su samu iznin jefa ƙuri’a ba, saboda dokar kotu ta haramta masu.
Daga cikin ƙuri’u 2322 da aka jefa, Ogbonnaya Onu ya samu ɗaya tal, sai Emeka Nwajiuba shi ma ɗaya tal ya samu. Dama kuma ko filin gangamin zaɓen bai je fa.
Yayin da ministocin huɗu su ka rasa muƙami kuma su ka rasa takara, su zuma zaɓaɓɓun da ke kan mulki waɗanda ba naɗi ba ne, duk da sun faɗi zaɓe, sun ci gaba da riƙe muƙaman su.
Irin waɗannan sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, Gwamna Udom Emmanuel, David Umahi, Aminu Tambuwal, Bala Mohammed da Nyesom Wike.
Akwai irin su Gwamna Kayode Fayemi wanda shi ma ya na ciki, amma ya janye wa Tinubu.
Rotimi Amaechi:
Ko Buhari Zai Sake Ba Ɗan Amanar Daura Riƙon Amana?:
Rotimi Amaechi mutum ne da ya ci ribar dimokraɗiyya sosai, domin tun daga 1979 ya ake damawa da shi a jiha, har ya zama Gwamnan Jihar Ribas, tsawon shekaru takwas, daga 2007 zuwa 2015.
Daga 2015 kuma Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta APC, ta naɗa shi Ministan Harkokin Sufuri, muƙamin da ya riƙe tsawon shekaru bakwai.
Amaechi ya ajiye muƙamin Ministan Sufuri, ya shiga siyasa, inda ya shiga takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Amaechi ya gwabza zaɓen fidda gwani shi da ‘yan takara 17, bayan wasu bakwai sun janye a ranar zaɓe.
Ya yi ƙoƙari sosai, domin ya zo na biyu, amma ya samu ƙuri’u 316 kacal. Yayin da wanda ya yi nasara, Bola Tinubu ya samu ƙuri’u fiye da dubu ɗaya.
Masu fashin baƙin siyasa na fassara Amaechi da cewa ya yi tunanin zai samu ɗaurin gindi daga Fadar Shugaban Ƙasa, domin ya samu takara.
Shi kan sa Amaechi ya yi wasu abubuwa da su ka bai wa da dama mamakin cewa duk share hanyar neman takarar shugaban ƙasa ne ya sa Amaechi ya yi su.
Misali ya kai aikin gina Jami’ar Harkokin Fasahar Sufuri a Daura. Sannan kuma ya shiga, ya fita an naɗa shi sarautar gargajiya ta Ɗan Amanar Daura.
Ganin yadda Amaechi ya dira filin zaɓen fidda-gwani gwani da ƙarfin sa, kamar wani ingarman doki, ya sa mutane sun yi tunanin akwai abinda ya taka.
Sai dai kuma bayan kammala ƙidayar ƙuri’u, Amaechi ya samu 316 kaɗai.
Amaechi ya karaɗe Arewa da sauran jihohin ƙasar nan ya na neman amincewar wakilan zaɓen ‘yan takara. Amma abin mamaki, 316 kaɗai ya samu.
Shin ya aka yi gwanin rawa ya faɗi? Wasu na cewa ‘deliget-deliget’ ne su ka juya masa baya.
Wasu kuma cewa su ke yi waɗanda ya dogara da su ɗin ne su ka canja masa fuska lokacin da zaɓen ya kusanto.
Yanzu dai Amaechi ba Minista, ba takara kuma babu naira miliyan 100 da ya sayi fam.
Abin da zai fuskanta a yanzu kuma shi ne Kwamiti Binciken da Gwamna Wike ya kafa masa, inda ake zargin sa da karkatar da fiye da sama da naira biliyan 80.
Godswill Akpabio: Ko Buhari Zai Sake Rungumar Sa Bayan Ya Yi Asarar Takara, Kujerar Sanata Kuma Ya Janyo Wa APC Hana Ta Shiga Zaɓen Gwamnan Akwa Ibom?:
Wannan bayani ne kan yadda Akpabio ya sauka daga minista, ya rasa takarar shugabancin ƙasa, kuma ya rasa takarar sanatan da ya nema don rage asara.
Tsohon Ministan Bunƙasa Yankin Neja Delta, Godswill Akpabio ya ɗibga asarar takarar ƙujerar sanata, wadda ya garzaya ya yi ƙoƙarin samu bayan ya rasa kujerar ƙarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC.
Akpabio na cikin ‘yan takara bakwai da su ka janye wa Bola Tinubu. Shi ne ya fara janyewa, shi ya sa a zaɓen bai samu ƙuri’u ko guda ɗaya ba.
Kafin Akpabio ya shiga takarar shugaban ƙasa, inda ya ajiye aikin sa na Ministan Harkokin Bunƙasa Yankin Neja Delta.
Bayan rashin nasarar sa ne sai ya garzaya jihar su a Akwa Ibom, inda a ranar Alhamis sai APC ɓangaren sa ta shirya zaɓen fidda gwani, aka ce shi ya yi nasara.
To sai dai kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta ce ba ta amince da zaɓen fidda gwani ba wanda aka zaɓi Akpabio, domin ko wakilan INEC ba a tura domin su kalli yadda zaɓen ya gudana.
“INEC ta amince da zaɓen da aka yi wa Akinimo Udorfia tun a ranar 28 Ga Mayu, a matsayin ɗan takarar APC na Sanatan Arewa maso Yamma na Akwa Ibom.
Akpabio ya sha fama da rikici shi da tsohon Sakataren Yaɗa Labaran APC, John Akpanudoedehe.
Akpanudoedehe shi ma ya fice daga APC, inda ya koma NNPP ya samu takarar shugaban gwamnan Akwa Ibom.
Ya fice daga APC ne bayan da aka ba wani sabon-shigar APC takarar gwamna a jihar, tun bai cika kwanaki 30 da shiga jam’iyyar ba.
To shin ko yaushe ne Akpabio zai wartsake? Wataƙila idan APC ta kafa gwamnati, Tinubu ka iya saka masa da muƙamin minista a 2023.
Akpabio ya shiga rikicin ‘ba gaira ba dalili shi da tsohon Sakataren APC na Ƙasa John Akpanudoedehe. a Akwa Ibom.
Wannan rikici ya haifar da jam’iyyar ta kasa gudanar da zaɓen fidda gwani na takarar gwamna na Akwa Ibom. Lamarin da INEC ta cire sunan APC daga takarar gwamnan jihar Akwa Ibom a zaɓen 2023 mai zuwa.