Ɗan takarar jam’iyyar APC na ƙasa, Bola Tinubu ya gode wa Shugaba Muhammadu Buhari dangane ta rashin tsoma bakin sa a zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar shugaban ƙasa.
A cikin wasiƙar wadda ya aika wa Shugaba Buhari, Tinubu ya ce ‘yan takara da shugabannin jam’iyya sun bai wa Buhari shawarar ya fidda wanda zai gaje shi.
“Har zuwa ranar 6 Ga Yuni, ranar da za a yi zaɓen fidda gwani, dukkan ‘yan Najeriya har da ni ɗin nan, mu na jira mu ji ka bayyana sunan ɗan takarar da ya fi kwanta maka a rai.
“Sai a tsakar dare lokacin da ‘yan takara su ka fara hawa su na gabatar da kan su ɗaya bayan ɗaya, na ƙara jinjina maka, ganin yadda tsaya a matsayin ɗan-ba-ruwa-na, ba ka goyi bayan kowa a cikin mu ba.”
A matsayi na wanda ya fara yin jawabi a wurin zaɓen, na zauna na saurari bayanan da dukkan sauran ‘yan takara su ka yi, ɗaya bayan ɗaya. Da tafiya ta yi nisa sai na fahimci dukkan mu gaba ɗayan duk ‘yan takarar ka ne, kowa na ka ne.”
Tinubu ya jinjina da irin kishin da dukkan ‘yan takarar su ka nuna. Ya ce a yanzu dai gaba ɗaya a haɗe ake, a dunƙule wuri ɗaya.
Tinubu ya ce ya na alfahari da rawar da Gwamnonin APC suka bayar wajen samun nasarar sa, haka gudummawar ‘yan Majalisar Tarayya da Sanatoci da sauran ‘yan jam’iyya baki ɗaya.
“Ba zan taɓa mantawa da gagarimar gudummawar su wajen samun nasarar zama ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC ba.”
Idan ba a manta ba, Tinubu ya aika wa Buhari wata doguwar wasiƙar kwanaki kaɗan kafin zaɓen fidda gwani, inda ya ƙara jaddada biyayyar sa ga Shugaban Ƙasa, bayan wasu kakkausan kalamai da Asiwaju ɗin ya furta akan Buhari.