Shahararren ɗan wasan finafinan Nollywood Jim Iyke ya karyata raɗe-raɗin da ake yadawa wai ya canja addini daga Kirista zuwa musulmi.
Jim Iyke ya ce ” Wanda ya yaɗa wannan labari bai yi min adalci ba domin ba haka abin yake ba. Ban canja addini na ba, bani da niyyar haka, kuma ba zai taɓa daruwa ba.
” Ba so in yi magana a kai ba amma na ga kamar abin na so ya zama abin surutu ne akai shine ya sa na fito domin in sanar wa duniya gaskiyar lamari.
” Ni mutum ne mai mutunta kowani addini, amma abinda ake yadawa ba haka bane. Bana runanin abinda ake yadawa zai taɓa faruwa ma.
Iyke kara da cewa ” Wani fim ne muka yi a kasar Ghana kwanannan wanda zai fito a watan Yuli. Fim ɗin ya ƙunshi abubuwan addini, shine wani wa ya tsattsakuro wasu hotuna daga cikin fim din ya rika yadawa wai na canja addini. Ba haka bane.
Discussion about this post