Yayin da ake ce-ce-ku-ce kan takardun makaranta da kuma tababar yadda takardun shaidar kammala makarantun Bola Tinubu su ka salwanta, kamar yadda ya yi wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa rantsuwar cewa an sace su, PREMIUM TIMES HAUSA ta auna takardun Tinubu ɗan takarar APC, Atiku Abubakar ɗan takarar PDP da kuma na Rabi’u Kwankwaso ɗan takarar NNPP.
A rantsuwar da Tinubu ya yi wa INEC a rubuce, ya ce takardun makarantun da ya halarta duk sun ɓace, an sace su.
Sai dai kuma shekaru 23 kenan Tinubu na cewa an sace masa takardun, amma zuwa makarantun da ya yi iƙirarin ya halarta domin ya karɓo sabbi, abin ya faskara.
Ya rattaba cewa ya yi firamare a Badun, ya kammala Digiri kan Harkokin Kasuwanci a Jami’ar Jihar Chicago da ke Amirka a ranar 22 Ga Yuni, 1979.
Tinubu ya ce ya yi bautar ƙasa (NYSC) cikin Nuwamba, 1982.
Shi kuma Atiku Abubakar, ya fayyace cewa ya yi Firamare ta Jada a Jihar Adamawa, sannan ya samu satifiket na kammala Sakandare cikin 1965.
Amma satifiket na Atiku, ya nuna sunan da aka rubuta Siddiq Abubakar.
Atiku ya nuna ya yi Digiri na Biyu a kan Hulɗar Dangantaka Tsakanin Ƙasa da Ƙasa, a Jami’ar Anglia da ke Birtaniya.
Atiku ya yi Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma ya yi aiki da Hukumar Kwastan, wadda ya bar su ya bayan ya yi ritaya cikin 1989 ya shiga siyasa.
Rabi’u Kwankwaso: Satifiket na Kwankwaso ya nuna ya yi Firamare ya kammala cikin 1968, ya gama sakandare cikin 1975.
Bayan Kwankwaso ya samu Horon Koyon Sana’ar Hannu, ya yi Difiloma da Babbar Difiloma, ya yi Digiri, ya yi Digiri na Biyu. Sannan kuma Kwankwaso ya zama Dakta a fannin Ilmi Mai Zurfi Kan Tsarin Injiniyan Ginin Manyan Madatsun Ruwa da Noman Rani a Jihar Kano.
Kwankwaso ya yi aiki da Hukumar Sanar da Ruwa da Inganta Noman Rani ta Jihar Kano tsawon shekaru 14.
Kwankwaso ya yi Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya, ya yi Gwamna tsawon shekaru takwas. Ya yi Ministan Harkokin Tsaro kuma ya yi Sanata shekara huɗu, daga 2015 zuwa 2019.
Dawurwurar ‘Sace Takardun Tinubu’:
Miskilar Gona Mai Ɓacewa Ranar Shuka: Tinubu ya shaida wa INEC cewa takardun sa na firamare, sakandare da jami’a duk sun salwanta.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta liƙa sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa su 16 tare da bayanan inda kowanen su ya yi karatu ko aiki ko wani riƙe muƙami.
Sai dai abin mamaki, INEC ba ta bayyana komai ba a wuraren da ya kamata a bayyana makarantun da ɗan takara ya halarta, a ƙarƙashin sunan Bola Tinubu.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC Bola Tinubu, ya ƙi aika wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC takardun shaidar ya kammala firamare, sakandare da jami’a.
Dama kuma haka ya taɓa yi wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa a 1999, lokacin da ya yi takarar gwamnan jihar Legas a ƙarƙashin jam’iyyar AD.
A wannan karo, Bola Tinubu bai ce komai ba. Amma dai ya rubuta wa INEC wasiƙar da ya haɗa da fam ɗin sa na takara, ya miƙa wa INEC. Wasikar na ɗauke da bayanin cewa:
“An sace min takardun makaranta na tun daga ma firamare har na sakandare da na jami’a, lokacin da na tsinci kai na cikin halin gudun hijirar tilas da na yi bayan Janar Sani Abacha ya hamɓarar da gwamnatin riƙon-ƙwarya a ranar 17 Ga Nuwamba, 1993.
“Kafin a hamɓarar da gwamnatin riƙon-ƙwarya a lokacin kuwa, ni ina Majalisar Dattawa ne, kuma ni ne Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗaɗe.
“Yayin da a lokacin bayan hawan Abacha mun matsa masa lambar neman ganin an dawo da dimokraɗiyya, ina cikin waɗanda aka kafa wa ƙahon-zuƙa, ana so a damƙe.
“Na gudu da yi gudun hijira a waje. Bayan na dawo cikin 1998, na taras an sace wasu muhimman kayayyaki na, ciki har da takardun shaidar kammala firamare, shaidar kammala sakandare da kuma kammala jami’a.”
A cikin takardar Tinubu ya rubuta cewa ya yi karatu a firamaren St. Paul Children’s Home School ta Ibadan a 1958 zuwa 1968.
Ya ce ya yi sakandare ta Government Collage Ibadan, 1965 zuwa 1965. Sannan kuma ya yi karatu a Kwalejin Richard Daley da ke birnin Chicago na Amurka. Kuma ya je Jami’ar Chicago.
Idan ba a manta ba, run cikin 1999 Tinubu ke fama da zargin kantara ƙarairayi a tsakardun makarantar sa.
An yi ta maka shi ƙara kotu a shekarun da ya ke Gwamnan Jihar Legas. A ƙarshe Ƙotun Ƙoli ta ce ba za a iya gurfanar da shi ba, saboda ya na da rigar kariya daga tuhuma.
Sabuwar Ƙara: Bayan Tinubu ya fito takara cikin watan Mayu ne kuma wata ƙungiya ta maka shi ƙara kotu, inda ta nemi a haramta masa shiga takara, saboda a cewar waɗanda su ka maka shi kotu, Tinubu ya yi ƙaryar kammala Jami’ar Jihar Chicago.
Har yanzu dai bayan ya lashe zaɓen fidda gwani, kotu ba ta ranar fara shari’ar ba.
Discussion about this post