“Wallahi, wallahi, wallahi ni dai kam ban ga wani banbanci ba, tsakanin Dan siyasa, ko ma’aikacin gwamnatin da zai sace dukiyar al’ummah, ya jefa al’ummar sa cikin halin ni-‘ya-su, da ‘yan kungiyoyin ta’addar Boko Haram, ISWAP, Ansaru da Barayin daji (kidnappers/bandits) da sauran su.
Basu da wani banbanci sam. Kai har ma gara wadancan ‘yan ta’addar da duk wani azzalumin da yake zama sanadiyyar jefa al’ummar sa cikin tashin hankali da ayukkan sa munana, ayukkan kazanta, ayukkan halin beraye, halin gafiya! Ya tara dimbin dukiya, wadda tafi karfin amfanin sa ko bukatar sa, kawai don yaji dadi shi da iyalan sa da ‘ya ‘yansa, alhali al’ummar sa kuwa suna ta tagayyara!
Ku sani, yaku ‘yan uwana masu girma, wadancan ‘yan ta’adda fa kawai zasu cutar da wanda kaddara ta fada a kan sa ne da ayukkan su. Su kuwa masu sace dukiyar al’ummah, gaba daya al’ummar suke halaka wa.
Sannan kuma ku sani, duk wadancan kungiyoyin ta’addanci da muke da su, suna addabar al’ummah, wallahi sun samu ne sanadiyyar ayukkan wancan barawon Dan siyasar, da wancan barawon ma’aikacin gwamnatin, da masu taimaka masu domin su aiwatar da wannan mummunar barnar, wadanda kuwa ana iya samun su a cikin ko wane irin jinsi na mutane: akwai masu taimaka masu a cikin ‘yan kasuwa, akwai su a cikin ma’aikata, akwai su a cikin jami’ai daban-daban, kai ina mai yi maku rantsuwa da Allah, har cikin malaman addini, na Musulunci da na Kiristoci, akwai masu taimaka wa gurbatattun can, domin a saci dukiyar al’ummah, a durkusar da al’ummah a dan sam masu wani abu! Kai har ma gasu nan a cikin kungiyoyin da aka kafa da sunan taimakon addini, amma cutar da addinin suke yi. Sun halaka al’ummah, sun rikitar da al’ummah, sun jefa rudani da tashin hankali cikin al’ummah, amma abin takaici, har yanzu bamu gane hakan ba.
Yanzu haka da muke gabatar da wannan taro namu mai albarka, ina mai shaida maku cewa, jinin wasu ‘yan uwan mu daga cikin wannan al’ummah yana nan yana ci gaba da kwarara; an saci wasu an shiga dasu daji, an kashe wasu, an kone motoci da dukiyoyin wasu, an hana jama’ah da dama zama a garuruwan su, ana yiwa matan mu da ‘ya ‘yan mu fyade, an tayar da dubunnan kauyukan mu sun zama kangaye, sun zama kufai, an talauta al’ummar mu da sunan biyan kudin fansa, an hana miliyoyin mutanen mu yin aikin gona, a jihar Kaduna da jihar Zamfara da jihar Katsina da jihar Niger da sauran jihohin arewa.
Amma duk da haka, abun kunya, abun mamaki, abun takaici, abun ban haushi, wallahi, yanzu haka da nike wannan bayani, wasu miyagu daga cikin wannan al’ummah, suna nan sun tare a garin Abuja, sama da sati biyu, da sunan addini, wai suna yiwa Bola Tinubu Kamfen. Suna nan suna ta kokarin roko da lallashin wasu jiga-jigai a cikin jam’iyyar APC da wasu Gwamnoni, wai akan dole-dole sai an bai wa Bola Tinubu ticket a jam’iyyar APC.
Kuma kuji fa, ina mai yi maku rantsuwa da Allah, duk suna yin wannan ne, ba domin maslahar al’ummah ba, a’a, suna yi ne kawai don maslahar kawunansu. Allah wadaran naka ya lalace! Ba komai, kuci gaba da yi, muna kallon ku, al’ummah tana kallon ku, kuma wallahi talakawa suna sane da duk wani danyen aiki da kuke aikatawa. Mutanen banza kawai!
Ba addini ne a gaban su ba, ba kuma arewa ce a gaban su ba, ba kuma al’ummar su ce gaban su. Sun sayar da mutuncin su da ‘yan kudi kadan, kuma suna neman su sayar da addinin Allah da al’ummar Annabi Muhammad (SAW), da ‘yan kudi kadan. Wallahi karyar-ku-tasha-karya! Kifi-na-ganin-ka-mai-jar-koma!”
Daga Imam Murtadha Muhammad Gusau