Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Ondo, Kassim Afegbua ya bayar da samarwa cewa zai fita daga PDP ɗungurugum, haushin Atiku Abubakar ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa matsayin mataimakin takarar sa ta shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Atiku dai ya gabatar da Ifeanyi Okowa a ranar Alhamis, a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023.
Afegbua wanda tsohon Kakakin Yaɗa Labaran tsohon Shugaban Mulkin Soja ne, Ibrahim Babangida, ya ce magana ta gaskiya Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ne ya cancanci zama mataimakin takarar Atiku a PDP, ba Okowa ba.
Wike ne ya zo na biyu, a zaɓen fidda gwani wanda Okowa ya sa ‘daliget’ na Jihar Delta baki ɗayan su suka zaɓi Atiku.
Afegbua ya ce Okowa ya ci amanar Wike ne shi ya sa Atiku ya saka masa mataimakin takarar sa.
Ya ce ai Okowa ne idan an tuna ya ɗauki nauyin taron ilahirin gwamnonin kudu na PDP a Asaba, inda aka zartas da cewa ɗan Kudu su ke goyon bayan ya zama shugaban ƙasa a 2023.
Afegbua ya ce Okowa ya ci amana, maimakon ya sa a zaɓi ɗan kudu Nyesom Wike, sai ya ci amanar Wike ya sa aka zaɓi Atiku, don dai kawai a naɗa shi ɗan takarar muƙamin mataimakin shugaban ƙasa.
A kan haka ne Afegbua ya ce zai fice daga PDP ya koma APC ya marawa Bola Tinubu, domin a tiƙa Atiku da ƙasa.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin dalilin da ya sa ya ɗauki Gwamna Okowa mataimakin takara.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana dalilan da su ka sa ya ɗauki Gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa ya yi masa takarar mataimakin gwamna a zaɓen 2023.
“Na yanke shawarar zaɓar mataimakin takara ne wanda tilas ya san irin halin taɓarɓarewa da lalacewa da rugu-rugun da gwamnatin APC ta yi wa wannan ƙasar.” Inji Atiku.
Atiku Abubakar ya zaɓi Ifeanyi Okowa domin kamar yadda ya ce wanda zai ɗauka tilas zai kasance ya na da masaniyar muhimmancin ilmi a cigaban zamani cikin al’umma, ta yadda za mu shirya matasa su riƙa yin gogayya da sauran ƙasashen duniya a zamanance.”
Sauran dalilan da ya lissafa sun haɗa da wanda ya ke da shauƙin ganin an ƙara haɗa kan Najeriya, kuma wanda zai taimaka masa a samu wannan nasarar.
Atiku ya nuna farin cikin yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani lafiya, kuma ya gode wa sauran ‘yan takarar da ya kayar, tare da sake neman haɗin kan su domin a tafi tare har a kai ga nasara.
“Kuma ina farin ciki da alfaharin fatan cewa idan na samu masarar zama shugaban ƙasa, to mataimaki na ne zai gaje ni. Don haka ya zauna da shirin shi ma Shugaba ne mai jiran gado.
“Kuma mataimakin takara ta zai kasance wanda a shirye ya ke ya taimake ni mu kawo ƙarshen matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan.”
Atiku ya ce tilas mataimakin sa zai kasance wanda zai taya shi dawo da ɗimbin masu zuba jari daga waje waɗanda su ka gudu daga ƙasar nan, yayin da gwamnatin APC ke barci har ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga masu ƙaryar su makiyaya ne su ka addabi ƙasar nan, da manoma da makiyayan ainihi.
Atiku ya ce ya saba ɗaukar matsayi mai wahala sosai. Don haka a yanzu ma sai da ya tsaya ya darje, bayan ya tuntuɓi manyan masu ruwa da tsaki sosai, sai ya ɗauki Ifeanyi Okowa.
Atiku ya ce a yanzu ba lokacin tsayawa surutai ba ne, jan aikin da ke gaban su shi ne tabbatar da cewa an yi nasara a zaɓen 2023.
Discussion about this post