Yayin da tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Tinubu ya yi nasara da ƙuri’u 1,271, wasu ‘yan takarar ko deliget ɗaya bai zaɓe su ba.
Tinubu na ɗaya daga cikin ‘yan takara 23 da su ka tsaya zaɓen fidda gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC a ranar Laraba, a Abuja.
Kowane ɗan takara ya sayi fam kan kuɗi naira miliyan 100. Amma bakwai daga cikin ‘yan takarar sun janye wa Tinubu kafin a kai ga jefa ƙuri’a. Akwai ɗaya da ya janye daga takara, amma bai ce ya goyi bayan kowa daga cikin sauran da ba su janye ba. Kenan ‘yan takara 14 ne su ka fafata.
Saukalen Rotimi Amaechi Daga Minista: Rotimi Amaechi ya sauka daga Ministan Harkokin Sufuri, ya shiga takara, ya samu ƙuri’u 316, kuma shi ne ya yi na biyu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya zo na uku da ƙuri’u 235, shi kuma Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya zo na huɗu da ƙuri’u 152.
Deliget uku daga kowace Ƙaramar Hukuma 774 ne su ka yi zaɓen.
Akwai ‘yan takara huɗu waɗanda ba su samu ko da ƙuri’a ɗaya tal ba.
Fasto Tunde Bakare, bai janye wa kowa ba, an fafata zaɓe da shi, amma ko wakilin zaɓe ɗaya bai zaɓe shi ba.
Bakare ya taɓa cika baki ya ce shi ne zai zama shugaban ƙasa na 16, idan na 15 wato Buhari ya kammala wa’adin sa a. 2023.
Rochas Okorocha, tsohon Gwamnan Jihar Imo kuma sanata mai ci a yanzu Sanata ne mai wakiltar Imo ta Yamma, ya je dandalin taro, ya yi magana da Hausa, Igbo da Turanci, amma ko ƙuri’a ɗaya bai samu ba.
Har gori ya yi wa sauran ‘yan takarar, “Ni Rochas Okorocha, Ɗanjikan Sokoto na fi sauran ‘yan takarar sanin matsalolin Arewa.”
Abin mamaki, yayin da ko ɗan Arewa ɗaya bai zaɓi Rochas ba, deliget 81 ma na Jihar Imo babu wanda ya zaɓi Rochas a cikin su.
Sauran waɗanda ba su samu ko ƙuri’a ɗaya ba, sun haɗa da Jack Rich da Ikeobasi Mokelu.