Shugabannin Jam’iyyar APC sun ce ba su goyon bayan a bai wa Sanata Ahmad Lawan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC kai-tsaye ba.
Sakataren Tsare-tsaren APC na Ƙasa, Suleiman Argungu ne ya bayyana haka.
Argungu da wasu mambobin kwamitin shugabannin APC su huɗu ne su ka yi wa manema labarai jawabi a ranar Litinin, biyo bayan rahotannin da ke nuna cewa wai an ɗauki Lawan a matsayin ɗan takarar da jarjejeniya ta amince da shi.
Amma kuma tabbatattun rahotanni sun nuna Shugaban APC Abdullahi Adamu ya ambaci amincewa da Sanata Lawan ɗin.
Sai dai Argungu ya ce batun wai an ɗauki Lawan ɗan takara, ba tabbataccen batu ba ne, domin ba a tattauna lamarin a wurin taro ba.
Ya ce kawai bayani ne daga bakin shugaban jam’iyya, amma ba daga uwar jam’iyya ba.
Ya ci gaba da cewa ai Abdullahi Adamu ya na da ‘yancin faɗar ra’ayin sa kamar kowa.
“Magana ce kawai ta fatar bakin Abdullahi Adamu, amma ba mu tattauna ta a wurin taro ba.”
Mu a matsayin mu na Shugabanni ko Kwamitin Gudanarwa, mu na goyon bayan matsayar da gwamnonin APC na Arewa su ka cimma, wato mun amince a miƙa takarar shugaban ƙasa a APC ga Kudu kawai.” Inji shi.
Discussion about this post