Idan ba a manta ba Sanata Ahmed Lawan wanda shine shugaban majalisar Dattawa ya fafata a zaɓen fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC rabar 8 ga watan Yuni.
A wannan zabe wanda Bola Tinubu ya yi nasara sanara Lawan ya zo na huɗu.
Kafin zaɓen an yi masa ƙyaƙƙyawar zaton cewa shina jam’iyyar ta ke so ta tsayar ɗan takarar ta amma kuma hakan bai yiwu ba.
Daily Nigerian ta buga labarin cewa wanda yayi nasara a zaɓen fidda gwani na kujerar sanata wacce Ahmed Lawan ya ke akai yanzu haka Bashir Machina ya ce ba zai sauka daga kujerar takara ba.
An shirya cewa idan ya faɗi zai koma ya amshi kujerar takara daga hannun Machina.
Machina yayi kememe cewa shi fa ba zai sauka daga kujerar takara ya mika wa Ahmed Lawan kujera ba, Shine ya fito takara kuma shi ya ci zaɓen fidda gwani.
Majiya ta shaida cewa Ahmed Lawan na so ya karbi wannan takara da ƙarfin tsiya tare da haɗin karfin kujerar mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin kudu maso gabas Salihu Mustapha.
Da aka tambayi Mustapha ko akwai wannan batu a gaban jam’iyyar sai ya ƙada baki ya ce, ” wannan matsala ce ta jam’iyyar a can gida bai shafi kasa ba. Ba hurumi na bane za su sasanta kansu a can gida.
” Idan ka duba za ka ga ko sanata Godwill Akpabio da yayi takarar shugaban kasa ya koma gida can Akwa Ibom an bashi takarar sanatan shi a APC.
Discussion about this post