Kotun Ƙolin Najeriya ta rattaba amincewa ɗaliban Najeriya mata Musulmai su riƙa zuwa makarantu sanye da hijabi a Jihar Legas.
Manyan Alƙalan Kotun Ƙoli bakwai ne su ka zartas da hukunci, inda biyar daga ciki su ka yarda cewa Musulmai mata na da ‘yancin shiga makaranta da cikin ajujuwa da hijabin su, yayin da biyu ba su amince da hakan ba.
Wannan ya sa hukuncin mutum biyar ya danne na mutum biyu kenan.
Manyan Alƙalan biyar dai sun jaddada hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta zartas cewa ɗaliban mata na da ‘yancin saka hijabi a cikin makarantun su.
Wannan dai shari’a ce wadda aka tafka tsakanin mai ƙara Asiyar Abdulkarim, ta hannun mahaifin ta, sai Moriam Oyeniyi da kuma Kungiyar Ɗalibai Musulmi ta Najeriya, waɗanda su ka maka Gwamnatin Jihar Legas kotu.
An fara shari’ar tun cikin 2014, inda Mai Shari’a Grace Onyeabo ta Babbar Kotun Jihar Legas ta jaddada amincewa da hukuncin da Gwamnatin Jihar Legas ta zartas cewa ta haramta saka hijabi a makarantu na firamare da kuma sakandare.
Sai dai kuma hukuncin da Babbar Kotun Legas ta yanke, bai samu amincewa ba Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Legas, inda kotun ta soke haramcin a ranar 21 Ga Yuli, 2016.
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana cewa kafa dokar haramta amfani da hijabi a makarantun sakandare da firamare ya tauye tare da danne haƙƙin ɗalibai Musulmi.
Gwamnatin Jihar Legas ba ta ji daɗin hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke ba, inda ita kuma ta garzaya Kotun Koli a cikin Fabrairu, 2017, a ƙarar da shigar mai lamba SC/910/16.
A ranar Juma’a ɗin nan ce Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa Jihar Legas ba ta da wani dalilin da zai sa ta kafa dokar haramta saka hijabi ga ɗalibai mata na firamare da sakandare.
Cikin manyan Alƙalan da su ka hana a haramta saka hijabi akwai Kudirat Kekere-Ekun da Tijjani Abubakar.
Sauran Alƙalan da su ka yi shari’ar sun haɗa da Olukayode Ariwoola, John Okoro, Uwani Baba-Aji, Mohammed Garba da Emmanual Agim.
Idan ba a manta ba, A.A Gumi na Kotun Ɗaukaka Ƙara ya zartas da cewa saka hijabi dama ce kuma tilas wadda addinin Musulunci ya wajibta wa mata Musulmai, don haka tauye masu damar tamkar tauye masu wani ɓangare ne na gudanar da ayyukan ibadar su.
Discussion about this post