Bankin Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya yi kakkausan gargaɗi ga Gwamnatin Najeriya cewa idan ba ta tashi tsaye ba, to babu makawa nan da shekarar 2026 gaba kuɗaɗen haraji da sauran kuɗaɗen shigar Najeriya zai riƙa tafiya wajen biyan basussukan da gwamnatin ƙasar ke tattagowa ne.
Wakilin IMF a Najeriya Ari Aisen ne ya bayyana haka a cikin wani rahoton da ya fitar ranar Litinin a Abuja.
Bayanin dai ya na ƙunshe ne a cikin Rohoton Halin da Tattalin Arzikin Ƙasashen Afrika ta Yamma ke ciki, wanda ya nuna tattalin arzikin Najeriya ya shiga garari matuƙar gaske matuƙa.
Ya ce a halin yanzu kusan kashi 89 na kuɗaɗen shigar Najeriya na tafiya wajen biyan basussuka ne.
“Sannan kuma duk wata Najeriya na kashe naira biliyan 500 wajen biyan kuɗaɗen tallafin mai. Wannan ma ba hanya ba ce mai kai kowace ƙasa tudun-mun-tsira.” Inji IMF.
Aisen ya ce idan Najeriya ta ci gaba da biyan kuɗaɗen tallafin mai har naira biliyan 500 a kowane wata, kamar yadda ta ke yi a yanzu, to zuwa ƙarshen shekara adadin abin da zata kashe wajen biyan tallafi zai kai naira tiriliyan 8 kenan.
“Gaba ɗaya kashi 100% na kuɗaɗen shigar Najeriya zai riƙa tafiya ne wajen biyan basussuka nan da 2026, in dai ba wani ƙwaƙƙwaran matakin saidaita tattalin arzikin ƙasar gwamnati ta ɗauka ba.”
Idan ba a manta ba, IMF da Babban Bankin Duniya sun sha shawartar Najeriya cewa ta daina biyan tallafin mai.
Discussion about this post