Jami’an tsaro sun cafke wani boka mai shekaru 70 Chukwujekwu Onuorah da ake zargi da laifin guntile kan dan majalisar dokokin jihar Anambra Okechukwu Okoye.
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Okoye Wanda ke wakiltan Aguata tare da darektan kamfen din sa a watan Mayu.
An tsinci kan Onuorah a tashar mota na Chisco dake kauyen Amichi dake karamar hukumar Nnewi ta Kudu gangar jikin kuma a kauyen Nnobi dake karamar hukumar Idemili ta Kudu.
Kungiyar kare rajin dan Adam ‘International Society for Civil Liberty and Rule of Law’ ta bayyana cewa jami’an tsaro na SSS sun kama boka Onuorah a kauyen Unubi dake karamar hukumar Nnewi ta Kudu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Tochukwu Ikenga ya bayyana cewa jami’an tsaro sun dade suna shirya yadda za su kama wannan kasurgumin boka.
Sai dai Ikenga bai bada bayanai yadda jami’an sa suka kama wannan boka ba.
Discussion about this post