Sunan ‘Dalaget’ – wato wakilan jam’iyyun siyasa – domin yanzu a kaf Najeriya, ba bu lungu da sakon da bai zagaya ba; ba bu kuma mutumin da yake bibiyar al’amuran siyasa da bai san irin tasirin da suke dashi ba wajen tsayar da dan takara a kowace jam’iyya ba.
Harma, yanayin yadda sunayen wadannan mutane yayi shuhura a wannan shekarar da al’umar Najeriya suke shirye-shiryen gudanar da babban zaben shugabanni na shekarar 2023, ya sha bam-ban kwarai – sakamakon yadda aka fito fili; aka bayyana irin tagomashin da yan siyasa suke ba su domin su zabe su.
Duk da cewa cinikin da su ‘dalaget’ din suke yi, za’a iya kiran sa da “cinikin zango-zango” – sabida ba ciniki ne da suke yin sa akai-akai ba, amma irin kallon irin yawan kudaden da suke samu ya janyo har mutanen gari suke sha’awar zama ‘dalaget’ su ma a nan gaba.
Wane ne “Dalaget” ma tun farko?
Dalaget shine mutumin da yake a matsayin halastaccen mamba na jam’iyyar siyasa, wanda sauran mambobin jam’iyyar da yake ciki suke zabar sa a matsayin wanda zai wakilce su wurin zabar dan takara daya tilo, da za’a kadawa kuri’a ranar zaben fitar da gwani.
Shine mutumin da yake haduwa da sauran yan’uwansa ‘dalaget-dalaget’ domin zabar dan takara – kuma duk wanda yafi samun kuri’u; shine wanda jam’iyya za ta tsayar a matsayin dan takara. Kuma ana zabo mutum guda ne daga kowace karamar hukuma dake fadin kasar nan 774.
Abinda Ya Faru Da Dalaget Masu Aikin Baban Giwa
Duk da cewa akwai manyan mukaman da har yanzu ba’a yi na su zaben fitar da gwanin ba, amma na kwana-kwanan nan da wata jam’iyya tayi a tsakiyar kasar nan, ya ja hankalin jama’a sosai – sabida irin kudaden Amurkan da aka ruwaito an baiwa masu daraja ‘dalaget’ kafin zaben.
To amma, a bisa binciken da nayi akan lamarin cinikayyar ‘dalaget’ da yadda ake gudanar dashi a kasuwar bukatar kujerar mulkin kowace jam’iyyar siyasar Najeriya, an fi so ayi ta “Yadin-Bi-Yadin” wato hannu-da-hannu – ba wai a samu wani dan kayi-nayi da zai karbo; ya rabawa masu zabe abinda yake so ba.
Wannan shine yasa duk wani dan takara da yake son darewa kan kujerar mulki, a kowane mataki, yake bin wadannan mutane domin neman goyon bayan su – sa’annan kuma ya damka masu kudi; kp kuma wata kyauta mai gwabi, wanda za su dan dade sunaa jalaftawa. Sai, dai sabida yanzu kusan lamarin duk ya zama shi kansa ‘dalaget’ din wadansu mutane ake samu; su karbo kwanturagin aikin – sa’annan su zauna a daki; su tsara cewa “wane shine zai zama dalaget; wane ba zai zama ba…” akan samu matsalar rashin bayar da hakikanin kudin da ake bayar din: ko dai a ba su kadan; ko kuma a hana su gaba daya.
Irin wannan matsalar tana faruwa sosai, musamman idan aka yi rashin sa’a cewa wani dan takara yana neman kujerar shugabancin kasa da yankin Kudancin Najeriya, sa’annan kuma mutanen daya sani na Arewa b aba ma su karfin amana bane, sai su yiwa ‘dalaget’ din wayo; su tsakuro wani abu daga cikin abinda aka bayar – sauran su sanya su a aljihun su.
Ko a zaben kwanan nan da wata jam’iyyar siyasa tayi na tsayar da dan takarar ta, kafafen yada labarai da dama sun ruwaito yadda akayi ta zargin wani dan siyasar da karbar irin wadannan kudade domin rabawa wakilan jam’iyyar jiharsa da aka zaba domin kadawa dan takarar da yake so kuri’a – amma daga karshe sai ga bayanai sun fara fitowa cewa an yi masu kwange a harkar.
Wadannan fa sune mutanen da suka niki gari; suka rankaya zuwa wancan garin da aka gudanar da babban taron kada kuri’ar fitar dan takara a bisa tsan-tsar biyayya ga mutumin da ‘sam’ ba halastaccen dan cikin gida bane – amma sabida ance yana da wani lissafi…ya hakikance wajen yin uwa da makarbiya a lamarin gidan da ba nasa ba.
Yanzu dai da alama baya ta haihu, domin bayan komawar wadanan mutane ‘dalaget-dalaget’ da masanin hanya ya aike su a wancan birni, yanzu haka duk sun dawo aljihu ba bu nauyi kamar sauran wakilan jam’iyya na ragowar jihohin kasar – wadanda aka cikawa aljihu da kudaden Amurka…gas hi kuma tuni mutane sun fara aike masu da lambobin asusun bankunan su domin su ma kada a bar su a baya.
Abin tambayar shine, ina biyayyar da wadannan mutanen ta tafi – su da ake yabon sun iya Sallah; amma sai ga shi alwala ma tana neman gagarar su a bainar jama’a? Ko da yake, wannan ba shine abin tambaya ba da farko, domin yin bulaguro zuwa wancan gari mai nisa da hadari shiga – abu ne daya cancanci a baiwa mutum hakkinsa yana kamala aikin da aka sa shi. Amma “Namu Duka” ya hana; karshe ma ya nuna wa Duniya aljihunsa gaba daya; ya ce ba bu komai a ciki.
Abin tausayin ma shine yadda duk dinsu, har yanzu, suka gagara tunkarar “Namu-Duka” din domin jin bahasin yadda kudaden na su suka makale; bayan suna da tabbacin cewa Nakudu ya bayar da hakkokin su a damka masu – da zarar sun kamala aikin su. Amma wannan lamari sabida irin sarkakiyarsa, yana da bukatar mutum ya samu wuri mai kyau – kamar lambu – inda zai natsu; yayi tunanin yadda zai baiwa dalaget-dalaget din nan shawarar yadda za su kwato yan matsabban su a hannun Namu-Duka, tun kafin ya sulmiyar dasu cikin Kwando.
Tsautsayi dai ance “ba ya wuce ranar sa” domin yanzu kam wadannan wakilai ban da da sun sani; ba bu abinda suke yi – sabida sun tafi wancan birni da tunanin cewa dawa za tayi nama idan sun dawo; amma kuma da suka koma sai suka ji wayam…sabida Namu-Duka gaba daya hankalinsa yana kan gonarsa da yan Barema ke zuwa neman aiki – kuma idan bai mayar da hankali; ya zabi wanda yake ‘shuda-shuda’ ba, hankalinsa ba zai kwanta ba.
Su kuma, bama za su iya fitowa suyi Magana aji su a gari ba, sabida al’uma har yanzu daukar Namu-Duka suke yi a matsayin mai kishin al’uma; mai yin komai domin Allah.
Discussion about this post