Hukumar EFCC ta saki dakataccen Akanta Janar Ahmed Idris, wanda ta kama makonni uku da su ka wuce, bayan ta zarge shi da kantara satar naira biliyan 80.
Kakakin Yaɗa Labaran EFCC Wilson Awujeran ne ya tabbatar wa wakilin mu da sakin da hukumar ta yi wa Idris, a wani saƙon tes da yi masa.
“E, tabbas mun bada belin sa.” Saƙon da ya turo wa wakilin mu kenan a taƙaice.
Sai dai kuma bai sanar da wakilin mu irin sharuɗɗan belin da aka gindaya wa Akanta Janar ɗin ba, wanda a yanzu a dakace ya ke, an ma hana shi zuwa ofis.
EFCC ta kama Idris ranar 16 Ga Mayu a Kano, bayan an sha aika masa wasiƙar gayyata ya ƙi zuwa ofishin ya yi bayanin salwantar naira biliyan 80.
Majiyoyin mu sun tabbatar da cewa EFCC ta daɗe ta na binciken kuɗaɗen, waɗanda ta ce an karkatar da sama da naira biliyan 80 ta hanyar kwangilolin ƙarya.
Kamfanonin da aka riƙa damfara wa kuɗaɗen duk iyalan sa ne da makusantan shi Akanta Janar Ahmed Idris ɗin ne. Haka dai wani mai bincike ya tabbatar.
Tuni dai aka dakatar da Ahmed Idris, sannan aka hana shi duk wata mu’amala da ma’aikatan ofishin sa.
Discussion about this post