PREMIUM TIMES ta damƙe wasu sahihan bayanai masu ɗauke da dalla-dallar yadda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ya haɗa baki da Akanta Janar (AGF) su ka jidi naira biliyan 84, wadda EFCC ke ƙoƙarin ƙwaƙulowa daga hannun su a yanzu.
Masu bincike sun tabbatar da cewa, daga cikin naira biliyan 20 da Yari ya jida, ya yi bindiga da dala $700,000 cikin kwanaki kaɗan, a tafiyar sa Umra cikin azumi.
EFCC na binciken Ahmed Idris da Yari su ka jidi naira biliyan 84 cikin watanni 10, wato daga Fabrairu zuwa Nuwamba, 2021.
Yayin da an bayar da belin Ahmed Idris, shi kuma Yari har yanzu ya na tsare ana yi masa tambayoyi da bincike.
Masu masaniyar binciken sun ce kuɗaɗen da Ahmed da Yari su ka sata, sun kamface su ne daga kuɗaɗen kashi 13% bisa 100% na kason da ake ba jihohi takwas masu arziki man fetur.
An tabbatar da cewa Akanta Janar ya karkatar da naira biliyan 84 ta hannun wani kamfanin tuntuɓa na wani mai suna Gbenga Akindele. Sunan kamfanin Westgate Projects Limited.
EFCC ta ce ba wani aiki kamfanin Westgate Projects Limited ya yi ba, sai dai kawai an yi amfani da shi ne “an yi gadangarƙamar sata.”
Idris da Yari sun haɗa baki da wasu jami’an Hukumar Rarraba Wa Tarayya, Jihohi da Ƙananan Hukumomi Kuɗaɗe (RMAFC) da kuma wasu jami’an jihohin tara wajen handame kuɗaɗen da sunan gudanar da ayyukan tuntuɓa.
Majiya ta ce bayan an tura wa Akindele naira biliyan 84, sai shi kuma ya fara rabawa tsakanin waɗanda aka shirya gadangarƙamar satar da su.
PREMIUM TIMES ta kasa jin ta bakin Akindele, sannan kuma kamfanin na sa ko sunan sa ma babu a shafin yanar gizo.
‘Mugu Shi Ya San Makwantar Mugu:
Majiya ta ce Yari ya danne kashi ɗaya na kuɗaɗen, sai ya bai wa Akanta Janar Naira biliyan 22.
Yari ya tashi da Naira biliyan 20, yayin da jami’an Hukumar RFAMC Naira biliyan 16. Wasu maƙudan kuɗaɗen da ba a san ko nawa ba ne kuma, sai aka miƙa su ga jami’an jihohin da ya kamata a tura wa kuɗaɗen.
Masu bincike sun ce Yari ya karɓi na sa kason ta hannun wani mai suna Anthony Yaro, na wani kamfani mai suna Finex Professionals Services.
EFCC sun tabbatar cewa Yaro ɗan-koren Yari ne.
Yadda Abdul’aziz Yari Ya Yi Bindiga Da Naira Miliyan 290 Lokacin Umrah A Saudiyya -EFCC
Jami’an EFCC sun ce dala 700,000 ɗin da Yari ya kashe a Saudiyya, ta na daidai da Naira miliyan 290.
Kuma ya kashe su ne wajen biyan kuɗaɗen kwana otal, zirga-zirgar hawa jirage da sauran saye-sayen tsaraba na ba gaira babu dalili.
EFCC ta ce Yari ya tafi Umrah tare da ɗimbin hadimai, ‘yan’uwa da makusanta.
Kakakin Yari, Mayowa Oluwabiyi, ya ce ba zai yi magana ba, tunda batun ya na hannun EFCC.
A farkon makon nan Premium Times Hausa ta buga labarin yadda EFCC ta kama tsohon Gwamnan Zamfara, ta na neman ƙwaƙulo naira biliyan 20 a hannun sa.
Zaratan EFCC sun cumuimuyi tsohon Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari, ta yi awon gaba da shi, bayan an gano ya na da hannu wajen tara Akanta Janar Ahmed Idris kantara satar naira biliyan 80.
EFCC ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ta kama Yari a gidan sa da ke Abuja, bayan bincike ya nuna cewa ya jidi naira kusan biliyan 20 daga cikin naira biliyan 80 ɗin da EFCC ke nema wajen Akanta Janar.
EFCC dai ta kama Ahmed Idris ne cikin makon shekaranjiya, bisa zargin karkatar da naira biliyan 80 da aka ba shi amanar ajiyewa cikin kuɗaɗen Najeriya.
An damƙi Yari a ranar Lahadi a Abuja, kwanaki kaɗan bayan ya ci zaɓen fidda-gwanin Sanatan APC na Zamfara ta Yamma ba hamayya.
An dai yi cacikui da Ahmed Idris tun a ranar 16 Ga Mayu.
A cikin 2021 EFCC ta sha kama Yari bisa binciken yadda ya karkatar da biliyoyin kuɗaɗe, wato wasu daban ba waɗannan biliyan 20 da ake magana a yanzu ba.
Ya yi Gwamnan Jihar Zamfara daga 2007 zuwa 2019.
Discussion about this post