Ɗan takarar jam’iyyar PDP na zaɓen gwamnan Jihar Barno, Mohammed Jari, ya bayyana cewa an tsayar da shi takarar ce saboda al’ummar Barno sun tabbatar cewa shi kaɗai ne zai iya kayar da Gwamna Babagana Zulum da gwamnatin APC a Barno.
“Lokacin da na sayi fam na shiga takara a ƙarƙashin PDP, wasu makusanta na a Legas da Abuja da sauran garuruwa, sun kira ni su na cewa, “yanzu kai har fam za ka saya ka shiga takara da Gwamna Zulum”.
“Na ce masu ƙwarai kuwa, har ma na saya, kuma sai na kayar da shi.” Inji Jajari.
Jajari ƙwararren ma’aikatacin banki ne masanin hada-hadar zuba jari.
Ya ce zai kayar da Zulum, wanda ɗimbin mutane a ciki da wajen jihar ke ganin ya yi aiki tuƙuru a wannan shekaru uku da ya yi a kan mulki zuwa yau.
Sai dai kuma duk da irin yabo da jinjinar da ake yi wa Zulum, Jajari ya ce ayyukan da Gwamnan ya yi ba su taka kara sun karya ba, da har za a riƙa cewa ya ci gaba da mulki bayan 2023.
“Waɗanda ke wajen jihar Borno na ganin kamar kayar da Zulum abu ne da ba ma zai taɓa yiwuwa ba. Amma mafi yawan mu ‘yan Barno mun san kayar da gwamnatin Zulum abu ne mai sauƙin gaske, saboda babu wani abin a zo a yaba da ke gudana a jihar wanda Zulum ya samar.”
Jajari wanda matashin ɗan siyasa ne, wanda bai cika shekaru 40 ba, shi ne ya ci zaɓen fidda-gwanin takarar gwamnan Barno na PDP. Ya kada Mohammed Imam.
Jajari ya yi alƙawarin inganta tsaro da bunƙasa tattalin arzikin Jihar Barno idan ya yi nasara ya zama gwamna.
Sai dai ana ganin da wahala ya iya kayar da Zulum, gwamnan da kwanan nan ya ce ko an yi masa tayin mataimakin shugaban ƙasa ba zai karɓa, saboda farfaɗo da Jihar Barno ne abin da ya sa gaba.