Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PRP, Kola Abiola, ya bayyana cewa jam’iyyar su da shi kan sa za su samu gagarimar nasara a zaɓen shugaban ƙasa da za’a yi a 2023.
Kola ya ce PRP za ta maimaita irin gagarimar nasarar da mahaifin sa Mashood Abiola ya samu a zaɓen 12 Ga Yuni, 1993.
Ya yi wannan cika-bakin ne a lokacin da shi da dukkan ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar su ka karɓi satifiket na lashe takara daga hannun Shugaban PRP na ƙasa baki ɗaya, Falalu Bello.
Kola ya ce a shekarar 2023 ce mahaifin sa M.K.O Abiola zai cika shekaru cif da lashe zaɓen shugaban ƙasa na 1993. Don haka shi ma ya na da yaƙinin cewa zai yi nasara, kamar yadda mahaifin sa ya yi nasara a wancan zaɓen.
“Zaɓen shugaban ƙasa da za a yi cikin 2023 ya na tuna min da irin yadda jama’ar da ba su taɓa yin zaɓe ba, su ka riƙa yin tururuwa su na zaɓen jam’iyyar SDP, wadda mahaifi na ya fito takara shekarar 1993. To a 2023 za a maimata hakan a kai na da jam’iyyar PRP.
Ya ce idan har mutane za su iya yin tururuwar jefa ƙuri’a a wancan lokacin, to a wannan lokacin ma za su iya yi.
Ya ce PRP za ta yi ƙoƙarin ganin ta cike wawakeken giɓi da ratar da aka yi wa ɗimbin matasa wajen tafiyar da mulkin ƙasa.
Ya roƙi matasa a fito a yi tururuwar jefa wa PRP ƙuri’a a dukkan zaɓukan majalisar jiha, gwamna, Majalisar Tarayya, Sanatoci da zaɓen shugaban ƙasa.
Ya ce PRP ta yi rawar gani a lokacin zaɓen ‘yan takara, saboda ‘daliget’ ɗin ta sun kai 3,625.
“Babu ƙaramar hukumar da babu PRP na ƙasar nan. Mu na da ‘yan takarar gwamna har a jihohi 22. Sannan mu na da fiye da mutum 500 masu takarar muƙamai daban-daban a zaɓen 2023.”
Kola ya ce a tarihin kafa PRP, wannan ne karon farko da ta fi shiga zaɓuka daban-daban na jihohi da tarayya.
Ɗan takarar gwamnan Jihar Cross River, Usani Usani ya ce PRP na da ƙarfin da za ta iya lashe zaɓe a ƙasar nan.
Tun farko shugaban PRP Falalu Bello, ya ce PRP ta shirya tsaf domin samar da ingantaccen mulki a tarayya da jihohi daban-daban.