Bayan ganawar da gwamnonin Arewa na APC suka yi a cikin yammacin Asabar zuwa dare, sun amince shugabancin kasar nan ya koma kudancin Najeriya.
Gwamna Aminu Masari wanda shine ya gana da manema labarai bayan ganawar gwamnonin ya ce gaba dayan su gwamnonin yankin Arewa na Jam’iyyar APC sun amince mulki ya koma yankin kudu.
” Dukkan mu gwamnonin yankin Arewa na jam’iyyar APC sun amince mulki ya koma yankin kudancin Najeriya idan wa’adin shugaba Buhari ya cika.
” Bayan haka mun kuma jinjina wa gwamnan Jigawa Abubakar Badaru wanda bayan haka ya janye daga takarar.
Gwamnonin da suka saka hannu a wannan takardar amincewa sun hada da
Aminu Bello Masari Governor of Katsina State
Abubakar Sani Bello Governor of Niger State
Abdullahi A. Sule Governor of Nasarawa State
Prof. B.G. Umara Zulum Governor of Borno State
Nasir Ahmad El-Rufai Governor of Kaduna State
Muhammad Inuwa Yahaya Governor of Gombe State
Bello M. Matawalle Governor of Zamfara State
Simon Bako Lalong Governor of Plateau State
Senator Aliyu Wamakko Former Governor of Sokoto State
Dr. A.U. Ganduje Governor of Kano State
Senator Abubakar Atiku Bagudu Governor of Kebbi State