Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa jam’iyyar APC ba za ta shiga zaɓen gwamnan jihar Akwa Ibom ba.
Wannan kakkausar sanarwa na cikin rahoton da Kwamishinan Zaɓe na Tarayya na Jihar Akwa Ibom, Mike Igini ya aika wa Hedikwatar INEC ta ƙasa da ke Abuja.
Hakan ya zo ne makonni biyu bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa zai yi wahala APC ta shiga zaɓen gwamna a Akwa Ibom, saboda rikicin da ya ɓarke tsakanin magoya bayan tsohon Ministan Bunƙasa Yankin Neja Delta, Godswill Akpabio da tsohon Sakataren APC, Mike Ekpedhoedohe.
Igini ya sanar da Hedikwatar INEC cewa kwata-kwata APC ba ta gudanar da zaɓen fidda gwani ba a ranar 26 Ga Mayu, 2022.
“Jam’iyyar APC ba ta yi zaɓen fidda gwanin ‘yan takarar gwamnan ba a Jihar Akwa Ibom. Saboda a matsayi na na mai sa ido, na isa filin da za a yi zaɓen a Sheergrace Arena a Uyo, tare da Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Akwa Ibom, Andrew Amiengheme, daidai ƙarfe 6:45 na yamma. Amma ba mu ga ko mutum ɗaya a wurin ba.
“Mun yi zaman jira har ƙarfe 10:30 na dare, amma ba mu ga kowa ba.”
APC ta shiga rikici a Akwa Ibom, wanda har shi kan sa Akpabio ya rasa kujerar takarar sanata, bayan ya kasa yin nasara a zaɓen takarar shugaban ƙasa.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Godswill Akpabio ya sauka daga minista, ya rasa takarar shugabancin ƙasa, kuma ya rasa takarar sanatan da ya nema don rage asara.
Tsohon Ministan Bunƙasa Yankin Neja Delta, Godswill Akpabio ya ɗibga asarar takarar ƙujerar sanata, wadda ya garzaya ya yi ƙoƙarin samu bayan ya rasa kujerar ƙarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC.
Akpabio na cikin ‘yan takara bakwai da su ka janye wa Bola Tinubu. Shi ne ya fara janyewa, shi ya sa a zaɓen bai samu ƙuri’u ko guda ɗaya ba.
Kafin Akpabio ya shiga takarar shugaban ƙasa, inda ya ajiye aikin sa na Ministan Harkokin Bunƙasa Yankin Neja Delta.
Bayan rashin nasarar sa ne sai ya garzaya jihar su a Akwa Ibom, inda a ranar Alhamis sai APC ɓangaren sa ta shirya zaɓen fidda gwani, aka ce shi ya yi nasara.
To sai dai kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta ce ba ta amince da zaɓen fidda gwani ba wanda aka zaɓi Akpabio, domin ko wakilan INEC ba a tura domin su kalli yadda zaɓen ya gudana.
“INEC ta amince da zaɓen da aka yi wa Akinimo Udorfia tun a ranar 28 Ga Mayu, a matsayin ɗan takarar APC na Sanatan Arewa maso Yamma na Akwa Ibom.
Akpabio ya sha fama da rikici shi da tsohon Sakataren Yaɗa Labaran APC, John Akpanudoedehe.
Akpanudoedehe shi ma ya fice daga APC, inda ya koma NNPP ya samu takarar shugaban gwamnan Akwa Ibom.
Ya fice daga APC ne bayan da aka ba wani sabon-shigar APC takarar gwamna a jihar, tun bai cika kwanaki 30 da shiga jam’iyyar ba.
To shin ko yaushe ne Akpabio zai wartsake? Wataƙila idan APC ta kafa gwamnati, Tinubu ka iya saka masa da muƙamin minista a 2023.