A wata sanarwa mai tabbatar da Gwamnatin Tarayya da ta jiha ta kasa kare rayuka da dukiyoyin jama’a, Gwamnatin Jihar Zamfara ta umarci al’ummar jihar cewa kowa ya tashi ya mallaki bindiga domin ya kare kan sa daga hare-haren ‘yan bindiga.
Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai Ibrahim Dosara ya sa wa hannu, gwamantin jihar ta kuma umarci Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar ya riƙa bayar da lasisin mallakar bindiga ga dukkan wanda ya cancanta kuma ya ke na kishin yin amfani da bindigar a inda ya dace.
Gwamna Bello Matawalle wanda ya hau mulki a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya tuma tsalle ya koma APC shi da Kwamishinonin Jiha da ‘Yan Majalisa da Sanatoci.
Matawalle ya ce ya koma APC ne domin hakan da ya yi ne kaɗai zai kawo ƙarshen kashe-kashe da ɓarnar da ‘yan bindiga ke yi a jihar.
To sai dai kuma, maimakon kashe-kashen da farmakin ya ragu, a kullum lamarin dai ƙara muni ya ke yi.
Ba Jihar Zamfara ce ta farko bayar da damar jama’a su tanadi bindiga domin kare kai ba.
Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina ya bayar da wannan umarnin a baya, ganin yadda ‘yan bindiga su ka kassara yankuna da dama a cikin jihar da Shugaba Muhammadu Buhari ya fito.
Wani mazaunin garin Moriki dake jihar Zamfara, Ibeahim Awwal, ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa wannan sanarwa ya tada musu hankali, domin ina talaka zai samu kuɗin mallakar bindiga.
” Wannan abu ya kai makura, ace wai gwamnati ta fito kurukuru ta ce kowa ya mallaki bindiga ya kare kansa saboda ta gaza kenan. Allah wadaran naka ya lalace. Ina talaka zai saka kansa? ” In ji Awwal.
Discussion about this post