Ƴan bindiga sun yi garkuwa da jami’an lafiya uku da mace mai ciki a cikin kwanaki uku a jihar Zamfara.
Maharan sun yi garkuwa da mutanen a ranar Asabar da Talata.
A ranar Asabar da safe ‘yan bindigan sun yi awon gaba da likita dake aiki a babban asibitin koyarwa dake Dansadau a karamar hukumar Maru, Muhammad Mansur.
Maharan sun sace Mansur, ma’aikaciyar jinya da mai shara a asibitin yayin da suke tafiya tare a motar Mansur.
Shugaban kungiyar likitocin Najeriya NMA reshen jihar Zamfara Manor Bature wanda ya tabbatar da aukuwar abin wa PREMIUMTIMES ya ce ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutanen a kauyen Mashayar Zaki dake hanyar Magami zuwa Dansadau.
“Muna kira ga mutane da su saka likitan da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su cikin addu’a Allah ya ƙubutar da su.
Wani cikin ‘yan uwan Mansur da baya so a fadi sunan sa saboda tsaro ya ce tun tuni ‘yan bindigan ke kokarin yin garkuwa da Mansur amma ba su samu nasara ba.
“Sau biyu maharan na kawo farmaki asibitin sannan duk zuwan da suke yi basa samun Mansur a asibitin.
Ya ce maharan sun kira iyalin Mansur sannan sun bukaci a biya su naira miliyan 20 kafin su saki likitan.
Bayan haka ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matar shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi NULGE, Sanusi Isa.
Isa ya ce maharan sun afka gidansa dake Damba da misalin karfe 1:23 na safiyar Talata inda suka yi garkuwa da matarsa dake da tsohon ciki wata 9.
Ya ce yana zargin cewa maharan sun zo gidansa domin su yi garkuwa da shi ne amma da basu iske shi ba sai suka arce da matarsa.
“Maharan sun tsallako ta Katanga inda kafin su shigo dakina na boye a wani wuri da suka gaji da nema na Basu gani ba sai suka tafi da matata.
Isa ya ce har yanzu maharan ba su kira sa ba.
Discussion about this post