Mazauna kauyukan Duguri, Gwana and Pali dake karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi sun koka kan yadda ƴan bindiga suka hana su zuwa gonakinsu.
PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa ƴan bindiga sun afka wadannan kauyuka makonni biyu da suka wuce inda suka hana manoma zuwa gonakinsu ga shi kuma damina ya kankama.
Dajin Yankari na daga cikin maboyar ‘yan bindigan a jihar Bauchi sannan shigowar ‘yan bindigan jihar ya nuna yadda annoban aiyukkan ‘yan bindiga ke yaduwa daga jihohin yankin Arewa maso Yamma zuwa Arewa maso Gabashin kasar nan.
Zuwa yanzu labaran kisa ko garkuwa da mutane ya tsorata manoman dake kauyukan Futuk, Mansur, Makosa, Digare da Goborawa inda suka gwamnace su zauna a gidajen su da su je gona.
Mazaunan sun ce kamar yadda suke jin labari maharan kan kama mutane domin a biya kudin fansan sa.
‘Yan bindiga sun kashe mutane a kauyukan Pele, Salihawa da Sabongari sannan wasu da dama sun ji rauni.
Wani mazaunin kauyen Sabongari Garba Sabongari ya ce lamarin ya zama abin damuwa ga mutane musamman yanzu da aka shiga lokaci na damina kuma gashi babu manomin dake iya zuwa gona.
Garba wanda iyayensa suka biya makudan kudade domin fansar kanen sa da abokansa daga hannu ƴan bindiga ya ce idan har ba a dauki mataki ba hare-haren ‘yan bindigan zai kara wa mutane wahala baya ga wanda suke fama da ita a kauyukan su.
“Maharan sun yi garkuwa da mutum hudu daga gidan daya, sun Kuma kashe mace daya a Tunburu sannan da dama sun ji rauni.
Wani manomi mai suna Musa Fatuk ya ce suna da yawan gaske idan ba noma suka yi ba yaya za su ciyar da iyalan su.
Mutane sun ce za a yi fama da yunwa idan ba an kori ‘yan bindigan ba kafin damina ya wuce.