Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutum sama da 20 a kauyen Furfuri dake karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.
Maharan sun yi garkuwa da matan tsohon Akanta-janarɗin jihar Abu – Bello Furfuri a wanna dare na Lahadi da suka kawo farmaki garon.
Wata majiya shaida cewa kungiyar ‘yan sa kai sun ceto matan Akanta-janar ɗinda Hajia Khadija da Hajia Ade.
Amma majiyan ta ce ‘yan bindigan sun arce da ‘ya’yan sa biyu masu suna Zulaihat Abu – Bello da Zainab Abu – Bello sannan da wasu dake aiki a gidan na sa.
Furfuri kauye ne dake da nisan kilomita 10 daga garin Gusau.
Wani dake zama a Bungudu Abdullahi Shehu ya ce maharan sun afka gidan Akanta-jana da misalin karfe 11 na daren Lahadi.
Shehu ya ce tun da Abu – Bello Furfuri ya zama Akanta-janar din jihar Zamfara yake zama tare da iyalensa a kauyen Furfuri.
“Ga dukan alamu maharan sun zo ne domin su yi garkuwa da shi kansa.
“Maharan sun iso a lokacin da Akanta-jana din ke gida amma ma’aikatan gidansa sun taimaka masa ya gudu daga gidan.
“Maharan sun Kuma shiga gidajen dake kusa da shi inda a cikin gida daya sun saci mutum 8.
Discussion about this post