Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo, ya ce Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna ya sharara wa Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ƙarya, lokacin da ya shaida masa cewa Lamiɗo da wasu gwamnoni shida na PDP sun yi ƙoƙarin komawa APC a shekarun baya.
El-Rufai dai ya yi iƙirarin da Lamiɗo ya ƙaryata ne a lokacin ya ke yabon Amaechi a Kaduna.
Amaechi ya isa Kaduna ne a ziyarar da ya kai ta neman goyon bayan wakilan zaɓen ‘yan takarar APC a zaɓen shugaban ƙasa. A wurin ne El-Rufai ya ce:
“Bari na ba ku wani labarin tarihin ƙullewar zumunci na da Amaechi tun lokacin da ya na Gwamna.
“Lokacin da mu ka fara zaman tattaunawa da gwamnonin G-7 waɗanda su ka so ɓallewa daga PDP zuwa APC, ni da Amaechi da Nyako Gwamnan Adamawa na lokacin mu ka riƙa ganawa, har mu ka kai ga samun gwamnonin biyar da su ka yarda su shiga APC. Daga nan ne kuma guguwar ta fara canjawa.
Daga nan El-Rufai ya yi ta sheƙa bayanan da ya riƙa nuna irin ƙoƙari da ƙwazon da Amaechi ya nuna, duk kuwa da cewa a lokacin shi ma ya na PDP, kuma yanki ɗaya da shugaban ƙasa na lokacin, Goodluck Jonathan, wato yankin Kudu maso Kudu.
To sai dai Lamiɗo ya ce El-Rufai ya sharara ƙarya, labarin ɓallewar wasu gwamnoni su koma APC a 2015, ba daidai ya bayar da shi ba.
“Ko sau ɗaya ba mu taɓa zaunawa taro a matsayin mu na G-7 ba tare da El-Rufai.
“Kai, ko sau ɗaya ba mu ma taɓa zama har mu yanke shawarar wai za mu ɓalle mu koma PDP ba, ballantana har a ce wai wasu gwamnoni biyu sun noƙe, sun fasa komawa.
“To idan ma har wasu gwamnoni biyu sun noƙe sun ƙi ɓallewa ɗin, sai sun nuna amana kare ƙima da mutuncin su ne.
“Saboda haka na fito ne domin na yi wa kalaman zaramboton da El-Rufai ya sharara musamman a kan gwamnonin guda biyu.
“An kafa ƙungiyar gwamnonin G-7 ne don ƙara wa dimokraɗiyya inganci da nagarta a PDP, ba don tattauna batun komawa PDP ba.”
Lamiɗo ya ja kunnen El-Rufai ya guji yin bakin-ganga idan ya na maganganun sa.
Discussion about this post