Tsohon Ministan Harkokin Sufuri Rotimi Amaechi ya yi magana dangane da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a ranar Juma’a cewa tilas sai ya fuskanci Kwamitin Binciken da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya kafa masa.
Idan ba a manta ba, bayan cikar wa’adin Rotimi Amaechi a matsayin Gwamnan Ribas cikin 2015, bayan ya canja sheƙa daga PDP zuwa APC, wanda ya gaje shi Nyesom Wike na PDP ya kafa kwamitin bincike na zargin ragargaje fiye da naira biliyan 80 da aka yi wa Amaechi.
Tsilla-tsillar Amaechi Daga Wannan Kotu Zuwa Waccan, Neman Kada A Bincike Shi:
Jim kaɗan bayan kafa Kwamitin Binciken Gwamnatin Rotimi Amaechi, wanda Gwamna Nyesom Wike ya kafa cikin 2015, Amaechi ya garzaya Babbar Kotun Jihar Ribas, inda ya roƙi kotun ta hana gwamnatin Ribas binciken sa. Amma kuma bai samu nasara ba, kotun ba ta amince da roƙon sa ba.
Sai dai kuma Amaechi ya samu muƙamin Ministan Harkokin Sufuri a ƙarƙashin Gwamnantin Shugaba Muhammadu Buhari ta APC. Daga nan ya garzaya ƙara a Babbar Kotun Tarayya, inda ya nemi kotun ta hana Wike ya bincike shi.
Ya shaida wa Kotun Tarayya cewa Wike wanda tsohon yaron sa ne, da ya taɓa aiki a ƙarƙashin gwamnatin sa, ya kafa kwamitin ne kawai don ya wulaƙanta Amaechi, kuma ya ci masa mutunci kawai.
Babbar Kotun Tarayya ta ƙi karɓar uzirin Amaechi, ta yanke hukuncin cewa ya je ya fuskanci Kwamitin Bincike, idan ya na da gaskiya, sai gaskiyar sa ta fisshe shi.
Amaechi ya ƙi fuskantar Kwamitin Bincike, sai ya garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara. A can ma kotu ta ce masa ya koma ya fuskanci Kwamitin Bincike.
Bai haƙura ba sai ya garzaya Kotun Ƙoli. A Kotun Ƙoli an ƙi yanke hukunci fiye da shekaru biyar, har sai cikin wannan mako, bayan Amaechi ya sauka daga muƙamin Ministan Buhari na Harkokin Sufuri.
Tun cikin 2017 Amaechi ya garzaya Kotun Ƙoli, amma ba a yanke hukunci ba sai a ranar 2017 Ga Mayu 2022, bayan ya sauka daga muƙamin Minista.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Amaechi ya fitar a ranar Juma’a, ya ce “Hukunci da Kotun Ƙoli ta yanke cewa Amaechi ya koma ya fuskanci Kwamitin Bincike, ai ba ya na nufin a gaban kotu ne ake tuhumar sa ba.”
Ya ce Kotun Ƙoli ita hakan ta ce masa, kwamitin bincike ba kotu ba ce.”
Yayin da Kotun Koli ta yanke hukunci cewa Amaechi ya koma a bincike shi, ta ci shi tarar naira miliyan 1, saboda ɓata wa kotun lokacin ta.
Kafin kafa Kwamitin Binciken Rotimi Amaechi da Gwamnatin Ribas ta yi a 2015, gwamnan da ya kafa kwamitin kuma ya gaje shi, Nyesom Wike ya yi zargin cewa Amaechi ya riƙa gabzar kuɗaɗen ya na kashewa wajen kamfen ɗin APC da Buhari kafin ranar zaɓen 2015, bayan Amaechi ɗin ya fice daga PDP, ya koma APC.